Ba za mu iya aiwatar da ƙarin kaso 40 na kuɗin lantarki ba – PHEDC

Daga AMINA YUSUF ALI 

Kamfanin rarraba hasken lantarki na garin Fatakwal (PHEDC) ya bayyana cewa, sam ba zai iya ƙarin kuɗin lantarki zuwa kaso 40% ba a dai-dai wannna lokaci.  

Kamfanin ya ƙara da cewa, a yanzu haka sun samu nasarar yi wa kaso 57 na masu amfani da wutar mitoci, amma fa a cewar su har yanzu guda 285,000 daga cikinsu ba su da mitoci. 

Manajan Daraktan kuma babban jami’in zartarwar  PHEDC, Dakta Benson Uwheru, shi ya bayyana haka a garin Fatakwal a ranar Larabar da ta gabata a yayin taron ‘yan jarida na ranar bikin cika shekara guda cif da kamfanin ya fara aiki a ƙarƙashinsa.  

Uwheru ya bayyana cewa, PHEDC a halin yanzu ba za ta iya ƙara kuɗin lantarki ba a yankunan da take ba wutar lantarki ba. Kuma a cewar sa, har yanzu ba a ba wa kamfanin umarnin ya ɗabbaƙa dokar ƙarin ba. 

Uwheru ya ƙara da cewa, hukumar kula da wutar lantarki, NERC, har yanzu ba ta nemi su yi ƙarin ba, har yanzu tana amfani da tsohon tsarin dokar biyan kuɗinta ne.  Don haka a cewar sa, shi ya sa har yau suke amfani da tsohon tsarinsu. 

Kuma a cewar sa, sun sanya jin ƙai a harkar kuma suna nuna tausayawa da nuna amana da kuma tallafa wa mutanensu. 

Kuma a cewar sa, kamfanin PHEDC ya samu cigaban da ya samu a cikin shekara guda saboda samun haɗin kai daga kwastomomi. 

A don haka ya ce suna godiya da fatan alkhairi ga dukkan abokan hulɗa/kwastomomi.

Domin a cewar sa, nasarar da suka samu a yau sun samu ne sakamakon jajirtattun abokan hulɗa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *