Ba za mu sake rattaɓa hannu da ASUU kan yarjejeniyar da ba za ta aikatu ba – Buhari

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ce, ba za su sake rattaɓa hannu da Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) kan yarjejeniyar da ba za ta haifar da ɗa mai ido ba.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne sa’ilin da yake gabatar da kasafin 2023 ga Majalisar Tarayya a ranar Juma’ar da ta gabata a Abuja.

Da yake jawabi, Buhari ya ce an ware wa malaman jami’a kaso mai tsoka daga kasafin da ya kai sama da biliyan N450 domin cim ma buƙatunsu.

Shugaban ya ce gwamnati na sa ran malaman jami’o’i su fahimci halin da ƙasa ke ciki a wannan lokaci.

Ya ƙara da cewa, a bayyane yake gwamnati ita kaɗai ba za ta iya ci gaba da ɗaukar ɗawainiyar fannin ilimin ƙasar nan ba.

Don haka ya ce akwai buƙatar samar da hanyayoyin da za su taimaka wa gwamnatin wajen samar da kuɗaɗen da kasafin ya ƙunsa.