Ba za mu yarda da ƙarin farashin man fetur ba – Ƙungiyar Ƙwadago

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Ƙwadago ta ƙasa, NLC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi watsi da shirin qara farashin man fetur a Nijeriya.

Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamared Ayuba Wabba ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Abuja a ranar Alhamis da ta gabata.

 A cewar sa, Manajan Darakta na Kamfanin Man Fetur na Nijeriya, NNPC,  Mele Kyari, ya sanar da cewa farashin man fetur zai iya yin tashin gwauron zabi har Naira 340 daga watan Fabrairun 2022.

Amma da ya ke mayar da martani ta sanarwar, Mista Wabba ya bayyana matakin da Gwamnatin Tarayya ta ɗauka na cewa za ta riƙa baiwa ‘yan Nijeriya miliyan 40 Naira 5,000 a matsayin abin da zai rage musu raɗaɗin illar ƙaruwar farashin man fetur da cewa babu hikima a ciki.

A cewarsa,  jimillar kuɗaɗen da gwamnatin ta ce za ta riƙa baiwa ‘yan ƙasa ya zarce kuɗaɗen da ta ce ta na kashewa a halin yanzu kan tallafin man fetur.

Shugaban na NLC ya ce duk wani yunƙuri na kwatanta farashin man fetur a Nijeriya da sauran ƙasashen duniya zai zama kuskure ne, inda ya suffanta yanayin da cewa, “kamar ka kwatanta tuffa da mangwaro ne.”

Manhaja ta rawaito cewa tuni ‘yan ƙasa dai su ke ta tofa albarkacin bakinsu a kan wannan batu na ƙarin man fetur ta kafafen sadarwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *