Ba za mu yi ƙarya don kare muradun gwamnati ba – Ministan Labarai

Daga BASHIR ISAH

Ministan Labarai da Wayar da Kan ‘Yan Ƙasa, Muhammad Idris Malagi, ya bayyana cewa ma’aikatarsa ba ta buƙatar sharara ƙarya don kare muradun gwamnati, “za mu riƙa faɗin komai yadda yake”, in ji shi.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da ya kama aiki bayan rantsar da shi da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi a ranar Litinin.

Ya ce ma’aikatarsa da gwamnati za su zama masu gaskiya wajen bada bayanai.

Ya ƙara da cewa, gwamnati za ta kasance mai ƙoƙarin yin gyara a duk inda ta yi kuskure.

Haka nan, ya ce nan ba da daɗewa ba za su fitar da tsare-tsaren da za su yi aiki da su tare da bayyana su ga ‘yan ƙasa.

Daga nan, Malagi ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su guji yaɗa labaran ƙarya, sannan su zamo masu tantance bayanai kafin yaɗawa. Yana mai cewa, ƙofar Ma’aikatarsa za ta kasance a buɗe ga ‘yan ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *