Ba za’a a taba mantawa da gudunmawar Domkat Bali ba- Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya aike da sakon taaziyya ga iyalan Janar Domkat Bali da daukacin jama’ar Plateau, kan rasuwa tsohon ministan tsaro na Najeriya, Janar Domkat Bali. Wannan sako dai ya fito ta bakin mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari ne, Malam Garba Shehu jiya juma’a a Abuja.

An hakaito cewa shugaban ya kira matar mamacin: Madam Esther, ya kuma nuna alhininsa gare ta, yan uwa, da abokan arziki, da kuma dukkanin abokan aiki na babbar majalisar kolin soja ta kasar nan.

Shugaba Buhari ya yaba da irin gudunmowar da marigayin ya bayar, bayan gwagwarmayar da ya sha, tun daga mukamin karamin soja har zuwa shugaban rundunonin tsaro na kasar nan.

A cewar sa, irin sadaukar da kai da jarunta da Bali ya nuna, zai cigaba da naso a zukutan sojoji yan kabilar Tarok. Haka kuma ba za’a manta da irin gudunmawar da ya bayar ba, a dukkanin rundunonin da ya jagoranta.

Buhari ya yi addu’a ga mamacin na samun gafara a wurin ubangijin sa.

Tuni dai shugaban kasa Buhari ya hada wata tawaga, da babban ministan tsaro, Janar Bashir Salihi Magashi mai ritaya zai jagoranta. Domin zuwa gaisuwa ga gwamnatin jihar Plateau da kuma iyalin mamacin.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*