“Masu satar fasaha ne matsalar marubuta”
Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Tun bayan rasuwar irin su Marigayi Yaron Malam da Abdul’aziz Sani Madakin Gini, rabon da ka ji wani jajirtaccen marubucin labaran yaƙe-yaƙe kamar tauraron adabinmu na wannan mako. Faisal Haruna Hunƙuyi, na daga cikin tsirarun marubuta labaran yaƙe-yaƙe da suka rage a duniyar marubuta adabin Hausa, suna nishaɗantar da masu karatu. ɗan asalin ƙaramar Hukumar Kudan a Jihar Kaduna, marubuci Faisal, ƙwararre ne akan harkar noma da kiwo, kuma ɗan kasuwa, yana da matuƙar sha’awar harkar karatu da rubuce-rubuce. A tattaunawar sa da wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu, ya bayyana asalin abin da ya zaburar da shi ga samun azamar karance-karance.
MANHAJA: Za mu fara da jin cikakken sunanka da abubuwan da kake gudanarwa na rayuwa.
FAISAL HUNƙUYI: Sunana Faisal Haruna Hunkuyi. Ni ma’aikaci ne kamfanin fitar da takin zamani na OCP Africa. Ina ɗaya daga cikin masu bai wa manoma horo da shawara a ɓangaren harkar noman zamani, sannan bayan kasancewa ta marubuci, ina kuma taɓa kasuwanci irin na busasshen kifi, da jaka irin na yara ‘yan makaranta da na zuwa anguwar mata.
Ko za ka gaya mana wani abu daga tarihin rayuwarka?
An haife ni a garin Hunƙuyi da ke ƙaramar Hukumar Kudan a Jihar Kaduna. Na fara karatun allo a wajen kakana sannan na fara Islamiyya a Hidayaturrahmaniyya Unguwar Sarki Hunƙuyi, kafin in wuce Makarantar Koyon Harshen Larabci ta Madrastul Kulliyatul Arabiyya Waddarasatul Islamiyya Basawa, Zaria. Na yi firamare da sakandire ɗina duk a garin Hunƙuyi, kafin in wuce Jami’ar Jihar Kaduna wato Kaduna State Uniɓersity, inda a nan na samu shaidar kammala digiri na farko a ɓangaren noma da kiwo tare da tsare-tsaren shige da ficen kayan noma, wato General Agriculture. Ina da aure da yaro guda ɗaya.
Wanne matakin rayuwa ko ƙalubale ka tsallake har zuwa matakin da kake a yanzu?
An tsallake ƙalubale masu tarin yawa kam, domin duk wani mai numfashi kullum cikin ƙalubale yake. Daga cikin ƙalubalen da na fuskanta yadda al’ummar da nake rayuwa cikinsu suka gaza wajen fahimtar wane ne marubuci da tasirinsa. Kasancewar na taso cike da son karance-karance tun daga na jaridu da mujallu har zuwa kan littattafan hikayoyi na Hausa da Turanci. Akwai wani da ba zan manta da shi ba kullum burinshi bai wuce ganin an muzantani a gaban a cikin aji ba don kawai ni makarancin littattafai ne.
Ire-iren waɗannan sun faru da yawa wanda a yanzu kuma na zama tamkar madubi a wajensu.
Ko za ka iya tuna abin da ya fara sa maka sha’awa kan karance-karance da rubuce-rubuce?
Karance-karance na fara shi tun ban wuce matakin firamare ba. Ina aji biyu na firamare zuwa aji uku, duk ajinmu ni ne a baya wajen rubutu da karatu. Akwai wani duka da malamin mu ya yi min, a lokacin akan karanta wani rubutun Hausa da na kasa, sannan ya sa aka yi min ihu a cikin aji. Daga nan fafutukar ta samo asali domin kafin mu gama aji huɗu na firamare, sai da aka kai ni na ke tashi a gaban aji in karanta littafin ‘Iliya ɗan Mai ƙarfi’ da su ‘Magana Jari Ce’. Abokina, shi ya fara zuwa mana da littafin yaƙi na Marigayi Yaron Malam. Sannan yayata ma’abociyar karance-karance ce ita ma. Idan ta ajiye na kan ɗauka in haye saman bishiyar da ke gidanmu ni ma in karanta.
Ina aji ɗaya a matakin sakandire na fara rubuta labarin yaƙi, wanda har yanzu yana nan a hannun abokina Jibril. Kafin in kammala aji uku na ƙaramar sakandire na rubuta labarai sun kai biyar. Wasu suna nan wasu ban san duniyar da suke ba.
Wanne tasiri harkar karatu da adabi suka yi ta hanyar inganta rayuwarka?
Ba ƙaramin tasiri harkar karatu da adabi suka yi a rayuwata ba. Domin silarsu ne na san abubuwa masu tarin yawa. Silar karance-karance ina iya kallon matsala da fuskoki mabambanta kafin in natsu in fitar da maganinta. A taƙaice adabi ya yi tasiri a gareni a fannonin zamantakewar rayuwa, kuma har yanzu akan doron ganin tasirin adabin nake.
Yaushe ka fara ƙirƙirar labari da kanka, kuma ko za ka iya tunawa da yadda labarin yake?
Na fara ƙirƙirar labarin yaƙi tun ina aji ɗaya na ƙaramar sakandire a lokacin na ba shi suna ‘Daren Mutuwa. Labarin wani jarumi da ke fafutukar neman wani zobe wanda ya yi alƙawarin kawowa masoyiyarsa. A kan hanyarsa ta neman zoben ne ya haɗu da wani tsoho ma’abocin addinin Musulunci ya amshi Musulunci a wajensa, cikin wani dare da ya zama daren mutuwarsa, silar harin samame da aka kawo masaukinsu. Samun labarin mutuwarsa ya harzuƙa masoyiyarsa wacce ta kasance ‘yar sarki kuma jaruma basadaukiya, ita ma ta ɗauki takobi ta sha alwashin ganin bayan duk wanda ke da hannu a mutuwar masoyinta. Kuma ba za ta yi kisa ba sai a cikin dare kamar yadda aka kashe sahibinta cikin dare.
Kawo yanzu ka rubuta littattafai ko labarai guda nawa?
Na rubuta dogayen labarai guda biyar da gajeru aƙalla guda goma sha bakwai. Littattafan da na rubuta ɗin kuwa su ne, ‘Makauniyar Zuciya’, ‘ƙamshin Mutuwa’, ‘Gobarar Kogi’, ‘Kisan Boko’, da kuma ‘Bokoti Mai Yoyo’.
‘Makauniyar Zuciya’, labarin wasu masoya ne da suka jima suna dakon soyayyar junansu sai da aka zo gaf da cikar burinsu, sai gwajin jinin ƙwayoyin halitta wato Genotype, ya kawo masu cikas. Tun daga asibitin suka lalata sakamakon da aka ba su, abokinsa da ya yi masu rakiya ya nuna masu illar ɓata sakamakon tare da tunatar da su abin da suke ƙoƙarin janyowa kansu, amma suka yi kunnen uwar shegu da nasiharsa. Sun ɓoyewa kowa har aka ɗaura musu aure. Rayuwar aurensu gwanin ban sha’awa har zuwa loƙacin da haihuwa ta fara yi musu sallama. Ganin sun haifi jaririnsu lafiya ƙalau suka sake samun lasisin cigaba da zama da juna, sai dai har zuwa lokacin da suka haifi yaro na biyu ɗauke da cutar amosanin jini, haihuwa ta uku ma ta zo da ciwon. ɗaya ya mutu ya bar ɗaya, tsananin talauci da wahalar rayuwa da uƙubar da yaran ke ciki ya sa mijin ya gudu ya bar matar da yarinyar a gadon asibiti, hakan ya harzuƙa iyayenta, har suka raba ta da tilon yarinyar da ke kwance tsakanin mutuwa da rayuwa. A ƙarshe dai sun dawo sun haɗu bayan wasu shekaru.
Shi kuwa littafin ‘Gobarar Kogi’ labari ne akan wani magidanci wanda ‘yan fashin daji tare da masu garkuwa da mutane suka sauya masa rayuwa daga ɗangata zuwa maragata. A taƙaice dai matsalar tsaro da hanyar magance ta cikin sauƙi shi ne maƙasudin abin da ke ƙunshe a labarin.
Akwai kuma labarin’ Kamshin Mutuwa’ Wanda labarin wani saurayi ne da ya haɗu da sharrin mijin abokiyar karatunsa. Sharrin da ya haɗu da shi kuwa, shi ya kusa zama almakashin tsinke zaren rayuwarsa, hakan ya haifar masa da cutar damuwa, wato ‘depression’. Mahaifiyarsa ce ta zama linzamin fito da shi daga cikin uƙubar da ya shiga ya dawo rayuwa kamar kowa.
Mene ne ya fi ɗaukar hankalinka wajen rubuta labari, kuma ta ina kake samun ilhamar tsara darussan labaranka?
Abin da ya fi ɗaukar hankalina in ji a raina yakamata in yi rubutu akai bai wuce in ga wata ‘yar ɓaraka a cikin al’umma wacce yakamata a wayarwa da mutane kai game da halin da suke ciki ba. Hakan ya sa gaskiya rubutuna a yanzu ya fi karkata kan zamantakewa da hanyoyin cigaban rayuwa ta fuskar zamani. Ina tsara darussan labaraina ne ta fuskar yadda jigon labarin ya zo min tare da yadda na ke son saƙon ya isa ga al’umma.
Yaya kake kallon gudunmawar da marubuta adabin Hausa ke bayarwa ga cigaban al’umma?
Marubuci wani mutum ne wanda yake nazari da binciken rayuwa da halayyar jama’ar da yake zaune tare da su, sannan kuma ya ɗabbaƙa rubutunsa domin fayyace ainihin daidaitacciyar hanya wacce kowa ya kamata ya bi. Marubuci yana da wata baiwa ta musamman da Allah ya ba shi, wacce da ita ne yake iya tsara maganganun da za su nusar da makarancin rubutunsa illar wani abu da ya yi masa karan tsaye a zuciya. Marubuci yakan yi tunani irin na mutane da dama, walau bai taɓa rayuwa a cikin su ba, ko kuma akasin haka. Marubuci wani madubi ne mai ɗauke da majigin nazarto wani abu da zai faru ko kuma ya taɓa faruwa a wani ƙarni na can baya, sannan ya iya hasashen abinda zai faru a gaba ma. Hange da kallon da marubuci ke yi wa al’amura shi ke ba shi damar amfani da hikima da fasahar shi wajen samar da mafitar abin da ake tunanin wanzuwarsa shekaru masu zuwa.
Shin kana shiga gasannin da ake shiryawa marubuta? A wacce gasa ka taɓa samun nasara, kuma da wanne labari?
Ina shiga gasannin marubuta sosai. Shiga gasa ita ma nasara ce a wajena, domin da a ce babu gasa da yanzu ban san wasu abubuwan da na sani ba. Sannan duk gasar da nake shiga babu wacce aka watsar da ni a kifawar farko sai an je zagaye na biyu, a hakan ma na kan fita cikin waɗanda ake karramawa. Kamar a shekarar da ta gabata, tun a farkon shekarar na shiga jerin waɗanda suka yi nasara a gasar ƙungiyar Hazaƙa Writers Association, Sannan labarina ya zo na huɗu a gasar Kyauta Daga Allah Foundation. Labarina yana cikin guda biyar ɗin da aka zaɓa a gasar Dala FM Kano a shirin Duniyar Marubuta. Akwai kuma labarina a jerin 15 ɗin da aka fitar a gasar Gusau Institute. Bugu da ƙari, akwai labarina a cikin labaran da aka karrama a gasar Hukumar Tace Finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano. A yanzu haka muna dakon sakamakon ƙarshe na gasar ɗangiwa Literary Competition, wanda akwai labarina a cikin 16 da suka yi nasara.
Shi ya sa a koyaushe nake cewa ‘Alhamdulillah’.
Yaya alaƙarka take da sauran marubuta?
Za mu fara da amsa wannan tambayar a mako mai zuwa, kafin wasu tambayoyin su biyo baya.