Ba zan iya rubuta waƙa ba har sai na yi bincike – Aliyu Al’usku 

Na gaje waƙa ne a wajen mahaifina

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Duk wani manazarcin adabi na sane da muhimmancin waƙa wajen raya al’adu da tasirinta ga ilimantar da jama’a. Don haka alaƙar waƙa da rubutu da wasan kwaikwayo take da tsohon tarihi, ba a ƙasar Hausa kaɗai ba, har ma da dukkan al’adu da ake nazarinsu a cibiyoyin ilimi. Malam Aliyu Usman Kuringafa, wanda aka fi sani da Aliyu Al’usku, ba ɓoyayye ba ne a fagen rubutawa da rera waƙoƙi cikin fasaha da zalaƙar harshe. A tattaunawarsa da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, mawallafin ya bayyana masa cewa shi waƙa a wajensa gado ce ba haye ya yi ba, kuma shi ma yana sa ran a cikin yaransa a samu mai gadon baiwarsa. Aliyu Al’usku, bayan kasancewarsa mawaƙi, kuma marubuci, yana da sha’awar zane-zane. 

MANHAJA: Ko za ka gabatar mana da kanka?

AL’USKU: As-salamu alaikum. Asalin sunana dai shi ne, Aliyu Usman Kuringafa, wanda wasu suka fi sani da ɗanlami. Ga masu bibiyar rubuce-rubuce da sauraren waƙoƙina kuwa sun fi sanina da Aliyu Usman Al’usku.

To, shi kuma sunan Al’usku daga ina ya samo asali?

Wato kamar yadda sunan ya nuna, Aliyu Usman Kuringafa, idan ka ciro haruffa biyun farko a cikin sunana, da na mahaifi da garinmu (AL + US + KU) su ne suka haɗu suka gina AL’USKU.

Gaya mana tarihin rayuwarka a taƙaice.

An haife ni a ranar 31 ga watan Yuli, na shekarar 1992, a garin Kuringafa, da ke cikin ƙaramar Hukumar ƙafur a Jihar Katsina. Kuma kasancewar gidanmu gidan almajirai ne, na fara karatun allo a hannun ƙanin babana Malam Umaru Gurgu, a nan ƙofar gidanmu.

Bayan nan an saka ni a makarantar firamare ta garinmu wato Kuringafa Model Primary School, inda na gama a shekarar 2003.

A shekarar 2003 ɗin ne kuma na tafi ƙaramar sakandire ta jeka-ka-dawo (Day) a garin ƙarfi, cikin ƙaramar Hukumar Malumfashi. Na yi aji uku a nan na gama a shekarar 2006. Daga nan kuma na tafi makarantar sakandire ta kwana a cikin garin Katsina, wacce ake kira da Katsina College, Katsina (K.C.K). Na yi nasarar kammala ta a shekarar 2009.

Daga nan kuma na dawo Kano da zama, inda na fara sana’a, da waƙe-waƙe, yayin da kuma na cigaba da karatuna. Na yi diploma a fannin sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa ta ƙwararru, wanda ake ce wa, Professional Diploma In Computer Studies, a Kwalejin Nazarin Ilimin Addinin Musulunci da Shari’a ta Aminu Kano, wacce aka fi sani da Legal Kano. Ita ma Allah Ya bani nasara na kammala a shekarar 2012. Na cigaba da harkokin kasuwanci da waƙoƙi gadan-gadan, tare da sauran al’amura na gwagwarmayar rayuwa, don samun damar rufawa kai asiri.

Na yi aure a shekarar 2014, kuma Allah Ya albarkacemu da yara, wasu sun rasu wasu kuma suna nan raye.

Ko za mu san waɗanne abubuwa ne ka samu zarafin gudanarwa a harkokin waƙoƙinka, da fannin adabi bakiɗaya, ko ake kan bayarwa?

A baya can ina yin zane-zane (Drawings), don a lokacin ma mutane da yawa har ni kaina na yi tunanin ta wannan fanni duniya za ta sanni. Duk da yake ko lokacin ina yin waƙar to, amma dai na fi mayar da hankali ga zane-zanen. Kodayake a lokacin ban ma wuce shekaru 10 ba a duniya. Kuma ina da karambanin rubutun labari duk da yake littattafan da na rubuta ba su fi uku ba, biyu na soyayya, ɗaya kuma na yaƙi. Sai dai kuma duk ban samu damar bugawa da kai su kasuwa ba. Daga karshe kuma dai waƙar sai ta samu rinjaye ta danne komai, har ya zama dai a kan rubutun waƙa da rerawa yanzu na tsaya.

Waɗanne abubuwa ne za ka iya cewa sun zaburar da kai wajen ba da lokacin ka kan rubuce-rubucen waƙoƙi da adabi?

Na wayi gari na ganni da baiwar waƙa ne, ina matuƙar son waƙa da zane-zane. Kodayake zan iya cewa na gaje ta ne a wajen mahaifina, wanda ya kasance sha’iri mai juya waƙoƙin Narambaɗa zuwa yabon Manzon Allah (S.A.W) kuma har yakan ƙirƙiri wasu nasa ma, to da na buɗe ido na ga hakan, sai kuma na ji ina sha’awar ni ma in dinga yi.

Kuma Alhamdulillah ga shi har yanzu haka dai ina cikin sha’aninta. Soyayyar da nake yi wa waƙa ta musamman ce, shi ya sa ta zama min ra’ayi, kuma farali, da na sa a raina, samu ko rashi a cikinta ba su hana ni yinta.

Waɗanne nau’i na waƙoƙi kake rubutawa?

Duk wani nau’i na waƙa ina iya yi. Walau rubutacciyar waƙa ko ta baka.

Kuma nakan taɓa kowanne ɓangare a cikin waƙoƙin yabon Manzon Allah (SAWA), waƙoƙin faɗakarwa da wa’azantar da al’umma, waƙoƙin soyayya da waƙoƙin aure. Harwayau, ina yin waƙoƙin taya murnar wani abin alheri, ko jaje ko ta’aziyya. Waƙoƙin siyasa, ko sarauta. Har ma ina rera waƙoƙin tallace-tallace da ake yaɗawa a kafafen watsa labarai. A taƙaice dai, ni mawaƙi ne da na karaɗe kowanne ɓangare, bani da shinge matuƙar ba waƙar saɓon Allah ba ce.

Za ka iya tuna waƙar ka ta farko da ka wallafa, kuma wa ya taimaka maka ka koyi rubuta waƙa?

Da kamar wuya! Duba da tsawon lokacin da na yi a fagen rubuta waƙoƙi da rera su. Shekaru sama da ashirin da ɗaya zuwa da biyu ba jiya ko shekaran jiya ba ne. Amma dai har yanzu nakan iya tuno da rera wasu daga cikin waƙoƙin na da yi a can baya tun ban kai shekaru 12 a duniya ba. Wasu ma ina da su a rubuce, amma dai bambance haƙiƙanin wacca ta rigayi wata ɗin ne da wuya, tunda a lokacin ba na saka kwanan wata da shekarar rubutawar.

Saurare da bibiyar waƙoƙin mawaƙa da nake nacin yi, amma dai a can baya babu wanda ya zaunar da ni don ya koya min yadda ake yi. Daga bisani kuma na fara samun damar mallakar littattafan koyon rubutun waƙa, tare da bibiyar rubuce-rubucen wasu mawaƙan, har ma da tambaya a kan abubuwa da ban fahimta ba.

Kawo yanzu ka rubuta waƙoƙi da labaran Hikaya guda nawa? Kawo sunayensu da saƙonnin da ke cikinsu?

Tirƙashi! To, a gaskiya dai kai tsaye ba zan iya iyakance waƙoƙin da na rubuta da rerawa ba. Amma dai ta tabbas waɗanda na rera za su kai sama da guda ɗari, rubutattun kuma za su kai sama da guda ɗari da hamsin, idan ka haɗe alƙaluman lissafin gabaɗaya, za su kai sama da guda ɗari biyu da hamsin kenan.

Wanne abu ka ke fara la’akari da shi kafin ka rubuta waƙa ko labari?

Abin da ya sa zan yi waƙar da kuma saƙon da nake son isarwa a ciki.

Yaya kake samun ilhamar yin rubutu, ko ƙirƙirar baitocin waƙa?

Ina samun ilhama ko in ce kari da baitoci ko ɗiyan waƙa ne ta hanyar tunanin da ya zo min a rai na yin ita waƙar. Kuma na kan faɗaɗa tunani da kuma dogon nazari a wasu lokuta ma har na kan ji yanayin yadda ni kaina abin ke taɓa zuciyata tun kafin ma in rubuta ko rera. Kuma na fi samar da karin waƙa da kyakkyawan tunani game da ita a lokacin da nake tafiyar ƙafa mai ɗan nisa, wasu lokuta ma don hakan nake tattakin. Ko idan ina tuƙa abin hawa musamman keke ko babur. Yanayin farinciki da na ɓacinrai duk nakan iya yin rubutu ko rera waƙa. Dare da rana duk ina yi a cikinsu, idan babu hayaniya ko wani sauti da zai ɗauke hankalina, musamman ma dai in akwai shayi (ruwan bunu) da ƙuli-ƙuli mai sukari a kusa, lokacin rubutawar (Dariya).

Wacce waƙa ce ta fara kawo maka ɗaukaka, kuma wacce ka fi samun alheri a kanta?

Waƙoƙi da yawa, kuma a lokuta mabambanta sun kawo min ɗaukaka. Amma dai waƙar ‘Alaƙar Tarbiyya da Tsaro’ ta fi kowacce, domin ta haɗa ni da mutane da yawa, manya da matsakaita, jami’an gwamnati da gamagarin mutane.

Ita dai wannan waƙar, ta buɗe min wani sabon shafin ɗaukaka da daraja a cikin mawaƙa da marubuta. Duk wani alkairi bai kai na tarin masoya da masu ƙarfafa gwiwa ba, ita kuma wannan waƙar ta tattare duk waɗannan abubuwa.

Wasu mawaƙa a yanzu ba su cika zama su rubuta waƙa ba, da zarar sun samu kari kuma amshi ya fita daidai sai kawai a shiga situdiyo a yi ta faman ƙaƙalo baituka, shin kai ma haka ka ke yi?

Ni kam ban ga abin gwaninta da har zan yi alfahari fa shi ba game da hakan. Hasali ma dai na kan raina tunani da darajar duk wani mawaƙi da na ji yana faɗar hakan. Ni kam sai na yi nazari, bincike sannan sai in rubuta, sannan kuma sai in rera. A wasu lokuta ma har na kan nemi shawarwari da kuma bai wa na gaba da ni su duba min, ko kuma su fito min da kurakurai ko wani ƙalubale da ka iya biyo bayan abin da na rubuta ko na rera. Ba kuma hakan na nufin masu dubawa ne za su sake min rubutun ba, a’a, sanar da ni za su yi, sai in je in gyara da kaina.

Me ya sa ka ke bai wa nazari da bincike muhimmanci a waƙoƙinka?

Waɗannan abubuwa farilla ne a gareni. Na ɗauke su da girma da mahimmanci da ba zan iya yin waƙa ba har sai na yi bincike, sannan kuma in rubuta. Ko aikin waƙar siyasa zan yi, sai na yi bincike a kan wanda zan yi wa waƙar. Haka waƙar aure da kuma ta jinjina bare kuma ta sarauta. Duk wanda ko abin da zan yi wa waƙa, sai na san wannan abu bakin gwargwadon yadda zan iya siffanta shi ga mai sauraro ko wanda yake karantawa. A taƙaice ni a wajena, babu yadda za a yi in iya waƙa ba tare da bincike da rubutu ba.

Kana da wasu masu rubuta maka waƙa ne kafin ka rera, ko kuma kai kake tsara komai da komai?

Tunda nake waƙa babu wani wanda yake rubuta min, sai dai ma ni in rubuta wa wasu. Duk waƙoƙin da na tsara ko na rera, ni ne nake yin komai da kaina.

Amma dai kamar yadda na faɗa a baya, nakan biɗi shawarwari da kuma neman ilmin abin da ban sani ba ga masana.

Me ya ja hankalinka da abokinka Abou Othaymin har ku ka rubuta waƙar marubuta?

To, gaskiya abubuwan suna da yawa, sai dai mafiya muhimmanci daga cikinsu su ne; son mu sanar da duniya wane ne marubuci, tasirin marubuta da kuma kaifin alƙalami da kuma rawar da rubutu yake takawa a cikin rayuwar kowanne ɗan’adam da yake rayuwa a doron ƙasa, kai har da matacce da wanda ba a haifa ba ma. Kuma Alhamdulillahi, kwalliya tana cigaba da biyan kuɗin sabulu.

Yaya marubuta suka karɓi waɗannan baitoci da ku ka tsara, kuma waɗanne kalmomin ƙarfafa gwiwa ku ka samu?

Duk da yake na sani ba tun yanzu ba, marubuta suna bibiya da yabon waƙoƙina, to amma tabbas wannan waƙa ta zo da rinjaye mafi girma a kan sauran waƙoƙina da suka fi so. Ba zan iya ƙiyasta adadin mutanen da suka yi mana fatan alkhairi da kuma godiyar wannan waƙa ba. Na sha jin wasu marubuta na cewa, “Na kasa rubutu tsawon lokaci, amma da jin wannan take da waƙa sai kuma tsumin rubutu ya motsa min.” Ko kuma ka ji suna cewa, “Sauraren taken marubuta da waƙar Alƙalami da Rubutu ya sa dole ne ma in tafi in yi typing.” Ire-iren waɗannan kalmomi ba kaɗan suke faranta min rai ba. Kai, akwai ma wata marubuciya da ta ce min jin wannan waƙar da take ya sa ɗiyarta ta lashi takobin gadon alƙalamin mahaifiyar tata. To, ko iyakar wannan ai sun isa mu samu ƙarfin gwiwa.

Kuma har yanzu muna ci gaba da samun ire-iren waɗannan kalmomi da jinjina daga mutane masu yawa daga marubuta da makaranta labaran Hausa, Alhamdulillahi kasiran.

Yaya ka ke ganin yadda ake martaba mawaƙi a cikin al’umma?

Mawaƙi mutum ne na daban ko in ce na musamman a cikin al’umma. Daraja, girmamawa da mutuntaka har ma da kyaututtuka da mawaƙi ke samu a cikin al’umma ya sha bamban da na sauran jama’a, kamar yadda muka sani. Kuma ina jaddada godiya ga Allah da Ya sa na zamo daga cikin mawaƙa. Tabbas ina alfahari da hakan kuma ban taɓa yin danasani a kan wannan ba.

Waɗanne nasarori ko ƙalubale aka fuskanta kawo yanzu, a cikin harkokinka na waƙa? 

Za mu ci gaba a mako mai zuwa, da yardar Allah.