Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Kylian Mbappe ya ce, ya sanar da ƙungiyar Paris St-Germain a cikin watan Yulin 2022 cewar ba zai zauna a ƙungiyar fiye da ƙarshen kakar 2024 ba.
Yarjejeniyar ɗan wasan mai shekara 24 za ta ƙare a ƙarshen baɗi da cewar za a iya tsawaita masa shekara ɗaya.
A baya ya aika wa ƙungiyar da wasiƙar cewar ba zai cigaba da buga wasa a ƙungiyar da zarar wa’adinsa ya cika a birnin Faris.
Kenan PSG za ta yi shirin sayar da Mbappe a kakar nan, idan ba haka ba za ta yi asararsa a matakin wanda yarjejeniyarsa ta ƙare a ƙungiyar.
Real Madrid ta daɗe tana bibiyar dan ƙwallon tawagar Faransa, wanda ya watsa mata ƙasa a ido da cewar ya zaɓi cigaba da buga wasa a PSG a bara.
Bayan da Karim Benzema ya koma buga wasa a Saudiyya, hakan na nufin Real na neman mai cin ƙwallo da zai maye gurbinsa, koda yake ana alaƙanta Harry Kane na Tottenham da cewar shi ne za ta ɗauka.
Mbappe, ya fara yi wa PSG wasannin aro a 2017 daga Monaco, daga baya ta sayi ɗan wasan kan Yuro miliyan 180, wanda yanzu ya ci ƙwallo 212 a wasa 260.