Babban ɗan Gwamnan Nasarawa ya riga mu gidan gaskiya

Daga BASHIR ISAH

Allah ya yi wa babban ɗan Gwamnan Jihar Nasarawa, Hassan A. A Sule, rasuwa.

Hassan ya rasu ne a ranar Alhamis inda ya bar duniya yana da shekara 36.

Sakataren Yaɗa Labarai ga Gwamna Abdullahi Sule, Ibrahim Addra ne ya tabbatar da rasuwar a sanarwar da ya fitar da safiyar Juma’a.

Sanarwar ta ce, “A madadin iyalin Mai Girma Gwamnan Jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, na sanar da rasuwar dansa, Hassan A.A Sule, wanda ya rasu ranar Alhamis, 26 ga Janairu, 2023.”

An shirya yin jana’izar marigayin ne da misalin ƙarfe 10 na safen Juma’a a garin Gudi da ke cikin Ƙaramar Hukumar Akwanga a jihar, kamar yadda sanarwar ta nuna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *