Daga BELLO A. BABAJI
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Ahmad Maƙarfi ya rasa babban ɗansa mai suna Faisal Ahmad Muhammad Maƙarfi.
Faisal ya rasu ne tare da wasu mutum biyu a yayin wani hatsari a kan babbar hanyar Zariya-Kaduna, a lokacin da suka taho daga garin Maƙarfi a daren ranar Asabar.
Wani mutum ya ce, Faisal ya rasa ransa ne a wani asibiti a lokacin da ake ƙoƙarin ceto rayukan waɗanda lamarin ya shafa.
Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamared Shehu Sani ya yi ta’aziyya ga iyalan mamacin game da rashin, ya na mai addu’ar samun rahama a gare shi, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.