- An haife shi a Oktoba, ya mutu a Oktoba
Daga BASHIR ISAH
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ya yi rashin babban ɗansa, Tunde David Mark.
Manhaja ta kalato cewar, Tunde ya rasu ne da safiyar Juma’a a London bayan fama da cutar daji.
Ana sa ran ɗauko gawar marigayin zuwa Nijeriya nan da ‘yan kwanaki don yi mata jana’iza.
An haifi marigayin ne a ranar 13 ga Oktoban 1971 inda ya bar duniya yana da shekara 51.
A halin rayuwarsa, marigayin ya yi karatu a gida da waje. Kuma ya mutu ya bar mata da ɗa ɗaya.