Babban buri na shi ne in gina gidan marayu – Fauziyya D. Sulaiman

Daga AISHA ASAS

Sunan ki sananne ne, sai dai jin tarihin ki ne abin buƙatar masu karatu.
Suna na Fauziyya D. Sulaiman. An haife ni a unguwar Fagge ta garin Kano a shekarar 1988. Na yi karatun Islamiyya a makarantar Maikwaru da ke Fagge da firamare ta ‘Festival Special Primary School’. Daga nan na tafi makarantar kwana ta ‘Yargaya inda na yi shekara uku, sannan na dawo makarantar ‘yan mata ta GGC Dala inda a nan na kammala karatu na. Daga nan na yi aure a 1999. A shekarar 2002 na koma karatu na yi difloma a ‘College of Hygiene’ a kan fannin lafiya, na kuma yi satifiket a kan girke-girke, wato ‘Hotel and Catering Services’, sannan na yi difloma a fannin da ya shafi na’urar kwamfuta. Na kuma yi kwasa-kwasai a fannin rubutu, musamman rubutun fim da kuma na littafi. Yanzu haka ina zaune a cikin garin Kano da yara takwas.

Za mu iya sanin sana’ar ki?
Gaskiya kusan a yanzu dai zan iya cewa ba ni da wata sana’a da ta wuce rubutu, kama daga rubutun littafi har zuwa rubutun fim, wanda shi ne ya ja ni zuwa gidan talbijin na Arewa24, wanda a nan ɗin ma rubutun mu ke yi, mu na rubuta shirin ‘Daɗin Kowa’, ‘Kwana Casa’in’ da kuma sauran finafinai masu dogon zango da ake haskawa a Arewa24 ɗin. Ina daga cikin marubutan da su ke wannan rubuce-rubucen. Saboda haka ni yanzu zan iya cewa rubutu shi ne sana’a ta tun bayan da na bar harkar lafiya wadda a da har shagon magunguna ina da shi, na kuma ɗan yi aiki na wucin-gadi a asibiti.

Rashin sana’a ga mata laifin su ne ko na mazajen su?
Rashin sana’a ba za a danganta shi a ce laifin miji ba ne, sai dai a ce laifin mata ne. Domin idan mace ta dage ta na son ta yi sana’a ko da maigidan ta mai taurin kai ne da zai hana ta, to akwai dabarun da za ta bi a matsayin ta na mace don ta ga ta shawo kan shi. To musamman kuma idan namiji ya samu mace da sana’ar ta tun ta na budurwa; saboda ni tun ina budurwa na ke sana’a ta. Na yi sana’o’i kala-kala kamar zovo, alawar madara da sauran su. Saboda haka a haka miji na ya same ni tun ina budurwa da sana’ar yi na.

Saboda haka idan mace ta na da abin yi zai yi wahala kuma namiji kai-tsaye ya ce zai hana ta yi, sai idan daga baya ne ta ce za ta yi. To ko ma dai menene, mace ta jajirce ta samu sana’a mai kyau wadda ba za ta shafi zamantakewar auren su na. Saboda haka ni ina ganin rashin sana’a laifin mace ce, domin idan har ba ta dage ba to ba za ta yi sana’ar ba.

Me za ki ce ga matan da su ke zaman kashe wando?
Matan da ba su da sana’a, su ke zaman kashe wando, zan iya kwatanta su da wannan waƙar ta Barmani Coge da ta ke ce wa “mace da ba ta sana’a aura ce”. Domin duk mace da ba ta da sana’a ta zama bora, ta rako mata duniya. Saboda a wannan zamani da mu ke ciki da mace ta ke dagewa ta na neman abin da za ta taimaki kan ta ta taimaki ‘ya’yan ta da maigidan ta; to idan ki ka zama ba ki da sana’a za ki zama ‘yar kallo ko da ke ce amarya ko uwargida. Duk matsayin ki, duk kuɗin mijin ki ya kamata ke ma ki tashi ki nemi na kan ki domin shi ne zai jawo miki mutunci. Idan kuma ki ka tsaya zaman kashe zani, to za ki zama borar da naira xaya za ta gagare ki. Abin da za ku ci kullum zai haɗa ki rigima da maigida, saboda yawan ba ni ba ni.

Ga ki marubuciya kuma mamallakiyar gidauniya mai taimakon al’umma. Shin ya ki ka iya haɗa taura biyu a lokaci guda?
To harkar rubutu da kuma harkar gidauniya wasu harkoki ne da su ka shigo cikin rayuwa ta da zan iya cewa kowane na zaman kan shi, amma kowanne na buqatar lokaci, sai dai yanzu kusan harkar gidauniya ta shafe rubutu na. A da ne na kan yi rubutun fim da na littafi duk a lokaci guda, amma shigowar gidauniyar sai ya janye hankali na saboda abu ne da ya shafi mutane sosai, al’umma ne da za su tunkare ka kullum kowanne da buqatar shi; wasu su zo gida na, wasu su yi min waya, wasu kuma su tare ni a kan hanya da sauran su. Saboda haka sai ta janye kaso hamsin cikin harkar rubutu na, ban da na Arewa24. Amma harkokin da yawa sai dai mu ce Allah ya ci gaba da dafa mana.

Yaya wannan gidauniyar taki ta faro?
To ita dai wannan gidauniyar ta fara ne da taimakon wani yaro mahaddacin Alqur’ani kuma ya na jan limanci, wanda shekarun sa ba su wuce ashirin ba. Ya na zaune a Fagge. Yaron ya yi fama da ciwon ƙoda. Sai abin ya ɓata min rai a lokacin, saboda an rasa kuɗin da za a yi masa wankin ƙoda. Saboda haka sai na ɗauka na saka a shafi na na Facebook na ce,

“Yanzu fisabilillahi duk faɗin Jihar Kano a rasa mutanen da za su taimaka wajen ceto rayuwar wannan yaro mahaddacin Alqur’ani mai girma?”

Da yake ina da mabiya sosai a shafi na, sai mutane su ka fara kira na su na cewa su na son taimakawa. A haka a haka har Mai Martaba Sarkin Kano a wancan lokacin, Sanusi Lamiɗo Sanusi II, shi ma ya tallafa sosai kan lamarin yaron. Amma daga baya yaron ya amsa kiran mahaliccin sa.

To daga baya ne sai mutane su ka dinga ba mu shawarar mu buɗe wannan ƙungiya ta ‘Creative Helping Needy Foundation’ wacce Allah ya albarkace ta da yin ayyuka mabambanta da ba za su lissafu ba tun daga lokacin da mu ka fara aikin mu zuwa yau.

Kin samu ƙalubale a tafiyar taki?
To ƙalubale kam dukkanin harkar da mutum zai yi ba ta rasa ƙalubale ba, sai dai ƙalubalen ba wanda za a sa shi a gaba ba ne a ce har ya kawo tsaiko tunda bai hana nasarar ta fito ba. Ƙalubale ne da mu ke samu daga wasu mutane da su ke can gefe da su ke mana wani irin kallo na hasashe. Yanzu akwai waɗanda su ke da niyyar taimakawa amma wasu su na gefe su na ganin abin da mu ke yi ba daidai ba ne; ko su na ganin ma bai kamata a ce za a yi wannan abin na taimaka wa mutane ta hanyar tara kuɗi ba, sai dai a bar mutane su ci gaba da shan wahala, kada a yi gidauniya.To wannan shi ne kusan ƙalubalen da zan iya cewa mu ke fuskanta a yanzu. Duk da yake dai mun yi kunnen uwar shegu da zantukan su, tunda waɗanda su ka yarda da mu su na ganin ayyukan namu.

Nasarori fa?
Nasarorin da mu ka samu su ne mun haɗu da mutanen da ba mu taɓa zaton za mu haɗu da su a duniya ba. Ta kai har za ka iya yin magana da matar shugaban ƙasa kai-tsaye, za ka iya magana da kwamishinoni, da ministoci da matan gwamnoni kai-tsaye, su kira ka su ce ga aiki ka yi musu ko kuma ga abu ka raba wa mabuƙata. Mata da manyan attajirai na Kano za su kira ka su ba ka abu su ce ka rarraba. Ban da kuma kyaututtuka na ban-mamaki da na ke samu, wanda yanzu ni ba zan iya kwatanta yawan abubuwan da na samu ba ta sanadiyyar wannan gidauniyar wanda mutane za su kira ni su ce kyauta ce ni su ka ba.

Sai kuma babbar nasarar da na ke alfahari da ita shi ne mun ɗauki ɗalibai su na karantar fannin likita, mu na biya musu kuɗin makaranta da komai da komai, kusan mutane huɗu; akwai waɗanda za su gama a wannan shekarar. Sannan kuma akwai yara ‘yan sakandare.

Bugu da ƙari, mun gina wa mata iyayen marayu sama da ashirin gidajen zama, mun kuma samar da ayyukan yi ga matasa, ga samar da ruwan sha a wasu ƙauyukan Jihar Kano da wasu jihohi, ban da masallatai da mu ka giggina. Gaskiya abubuwan ba za su lissafu ba.
Amma babbar nasarar ita ce faranta ran al’umma da mu ke yi.

Fauziyya

Wane kaya ki ka fi sha’awar sawa?
To a gaskiya ni dai na fi son sa atamfa, saboda ba na son kaya masu nauyi, amma idan wajen biki zan je na fi son sanya leshi saboda kamar ya fi karva ta; idan kuma ɗaurin aure ne a gidan mu na fi son in sa shadda.

Ɓangaren abinci fa, wanne ki ka fi son ci a rayuwar ki?
Ina matuƙar son tuwon shinkafa da kowace irin miya, kuɓewa ko kuka ko taushe. Zan iya yi miki kwana uku ina cin tuwo, musamman na shinkafa ba tare da ya gundire ni ba – in ci da safe, in ci da rana, in kuma ci da dare!

Ko Malama Fauziyya ta na ɗan taɓa siyasa ne?
Magana ta gaskiya ni dai Fauziyya D. Suleiman ba na sha’awar siyasa. Dalili na kuwa saboda ina ganin yadda ake butulci da cin amana da yaudara a cikin ta. Za ki ga mutane aminan juna amma a kan abu ƙalilan sai ki ga an zo an sava. To wannan abin ya na taɓa zuciya ta. Sam ba na jin daɗin in ga ana cin mutuncin juna saboda siyasa.

Matan da ke son yin sana’a amma ba su da jari, wace shawara za ki ba su?
Waɗanda su ke son yin sana’a ba su da jari shawarar da zan ba su ta farko ita ce su jajirce a kan abubuwan da su ka sa a gaba, sannan ana nemo hanyoyin da aka san za a samu ɗin. Misali idan ki na da iyaye ko miji, sai ki lallaɓa su har ki samu ɗan wani abu da za ki fara sana’ar ki, ko kuma ki na da wani abu da ku na ganin za ki iya ɗagawa ki sayar wanda zai iya yi miki jarin da ki ke so. Idan kuma babu ko ɗaya da ki ke da su, to sai ki nemi hanyar yin sana’ar hannu, kamar kitso ko wankau a wani gida da sauran makamantan su har ki iya samar da jarin abin da ki ke son yi.

Menene burin ki nan gaba a kan wannan gidauniyar taki?
Babban buri na nan gaba a gidauniya ta wanda Allah ya kusa biya min shi, shi ne in ga na gina gidan marayu wanda zan dinga ajiye ni ma nawa marayun, ina ajiye wanda ba shi da gata, mu samar mishi da abincin ciyarwa da suturu da makaranta. To gidan marayun mun kusa samar da shi da izinin Allah. Ba mu dai gina ba, amma mun samu filin. Ina fatan Allah ya cika min wannan buri.
Sannan kuma ina da burin gina makaranta ta marayu wacce ita ma za mu ɗauki nauyin su.

Wane kira za ki yi ga masu kuɗi?
Kiran da zan yi ga masu arziki ba ma su kuɗi ba – domin akwai bambanci tsakanin kuɗi da arziki, shi mai kuɗi ba lallai ya taimaka ba, amma mai arziki ya na iya bakin ƙoƙarin sa – to shi ne zan yi kira da su dinga kallon na ƙasa da su, su na taimaka masu. Duk da yake dai akwai ‘yan matsaloli ta ɓangaren su kan su masu neman taimakon, wani lokacin sai ka ji mutum ya fusata ka, ka ji kamar kada ma ka yi taimakon, amma laifin wani bai shafar wani. Saboda haka ina kira ga masu hannu da shuni su dubi na qasa da su, ko makwafcin ka ko ɗan’uwan ka idan bai da shi ka taimaka masa. Sannan irin waɗannan ƙungiyoyin namu ko da ba ka ba da kuɗi, za ka iya zuwa da kan ka ka ce a ba ka marasa lafiya guda kaza ka na son za ka taimaka masu.

Wasu idan ka yi masu zancen sana’a sai su ce gwamnati ba ta tallafa masu ba. Shin a matsayin ki na ƙwararriya a fagen bada tallafi, ki na ganin su na da gaskiya?
Wato gaskiya duk wanda ya ce zai tsaya jiran sai gwamnatin ta ba shi tallafi sannan zai nemi kuɗi to gaskiya zan iya cewa zai mutu da ciwon talauci, ko kuma zai mutu bai yi sana’a ba. Ga sana’o’i nan barkatai na matasa da qananan yara irin su ɗinki, saƙa, kanikanci da sauran su. Iyaye ya kamata su nuna wa ‘ya’yan su tun tasowar su, su tashi da sana’a.

To, mun gode ƙwarai da gaske.
Ni ma na gode. Allah ya ɗaukaka jaridar Manhaja.