Babban burina shine sama wa matasa aikan yi a ƙarƙashina – Zainab Ɗanƙasa

“Jajircewa ce maganin kowanne irin ƙalubale a sana’a”

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

A wannan makon filin Mata A Yau na fannin Gimbiya ya samu zarafin tattaunawa da wata jajirtacciyar matashiya mai suna Zainab Sani Mikai’l wacce aka fi sani da Zainab Ɗanƙasa, wacce ita ce shugaba kuma jagorar kamfanin Ɗanƙasa Dishes da ke Jihar Kano. A zantawarmu da wannan matashiya ta bayyana ma na yadda ta tsunduma cikin harkokin kasuwanci bayan kammala digirinta na farko a kan (Library Science and Information Technology) a jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano. Zainab ta ce babban burinta a rayuwa shi ne taimakon matasa da kuma ganin rayuwarsu ta inganta yadda za a dinga damawa da su a ɓangarorin rayuwa daban-daban. Sannan Zainab Ɗanƙasa ta ce, ita kam yanzu alhamdulillah domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu, la’akari da yadda ta ke samun cigaba a harkokin kasuwancin da ta ke yi. Ga yadda tattaunawar ta  kasance:

MANHAJA: Za mu so ki ba mu taƙaitaccen tarihin rayuwarki?
ZAINAB ƊANƘASA: Sunana Zainab Sani Mika’il wacce aka fi sani da Zainab Ɗanƙasa mamallakiya kuma jagorar kamfanin Ɗanƙasa Dishes. An haife ni a unguwar Ƙwalwa kwanar goda, na yi makaranta daga matakin ‘Primary’ har zuwa Jami’a inda na karanci ‘Library and Information Science’ a jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke Kano, haka kuma na yi makarantar islamiyya inda na samu kammala wasu daga cikin littafan addini.

A wacce sana’ar ce ki ka yi fice?
Kamar yadda kowa ya sani ina sana’ar girke girke wanda ya danganci abincin gargajiya, na zamani, ƙwalam da maƙulashe, abincin tarurruka da sauran su, haka kuma na kan taɓa sana’ar hijabai da takalma da kwalaben turare da sauran su.

Daga lokacin da kika fara zuwa yanzu wacce nasara kika samu a wannan sana’a?
Alhamdulillah an samu nasara mai yawa, musamman yadda matsayin sana’ar yake samun canji a kullum sai dai mu ce alhamdulillahi.

Waɗanne ƙalubale ki ke fuskanta a harkokin wannan sana’a ta ki?
To a kowanne kasuwanci dole a fuskanci ƙalubale, sai dai jajircewa ce maganin ko wanne irin ƙalubale a sana’a. Kamar haka ne mu ma a nan mu na fuskantar ƙalubale, sai dai alhamdulillahi mu na iya bakin ƙoƙari wurin shawo kan matsalolinmu. Babban ƙalubalen da mu ke fuskanta shi ne wajen turawa abokan cinikayyar mu abinda su ke buƙata, sai kuma matsalar ‘yan bashi.

Mene ne babban burinki a kasuwanci?
Babban burina a kasuwanci shi ne, na tallafa wa matasa wurin samun ayyukan yi a ƙarƙashina tare da taimaka wa iyaye da ‘yan’uwa da kuma abokan arziki. Haka kuma na tsaya da ƙafafuna.

Mene ne abin da ki ka fi so?
Abin da na fi so a rayuwa ta shi ne, karamci da tsayawa akan gaskiya.

To mene ne kuma abin da ba ki so?
Ba na son ƙarya, ba na son mai yin ta, haka ma ba na son mutum marar daraja mutane.

Wacce kala kika fi so a cikin kaloli?
A komai na fi son kalar fari, sannan ina son ‘Light blue’ da ‘pink’.

Mene ne kiranki ga matasa?
Baban kira na ga matasa shi ne, su tashi su nemi na kansu, domin samun ingantacciyar rayuwa.

Mun gode.
Ni ma na gode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *