Babban burina shine Tijjaniyya ta kafa jami’arta – Shehi Tijjani Auwalu

Daga BILKISU YUSUF ALI

Shehi Tijjani Sani Auwalu malamin masanin Islama ne kuma tsayayye, wanda ya kasance komai ya saka a gaba sai ya ga tabbatuwarsa. A ranar 24 ga Nuwamba, 2022, Majalisar Shura ta Ɗariƙar Tijjaniya ta tabbatar da naɗinsa a matsayin Shugaban cibiyar Majma’u Ahbabu Shehi Ibrahim Inyas na Ƙasa. Wakiliyar Blueprint Manhaja, BILKISU YUSUF ALI, ta samu tattaunawa da shi. Ga yadda hirar ta kasance:

MAHAJA: Mene ne taƙaitaccen tarihinka?

AUWALU: Sunana Tijjani ɗa ga Maulanmu Shehu Tijjani Sani Auwalu kuma ɗa ga Sayyada Aisha ‘yar Sheikh Ibrahim Niass. An haife ni a Kano a shekarar 1973. Mahaifina ya rasu ina ɗan shekara huɗu. Mahaifiyata sai ta koma Senegal aka bar ni anan Kano. Na fara zama a nan Darma Kano daga baya na koma Gyaɗi-gyaɗi gidan kakanmu Baba Amadu wanda Kawu ne ga Shehu Sani Auwalu. Na koma Gwammaja gidan Sheikh Usman Bashir da zama wanda a lokacin duk yaransa mata ne ba shi da yara maza kuma cikin hukuncin Allah ina zuwa ya fara samun ɗa namiji.

Karatunka fa?

Kamar yadda yake a ƙasar Hausa, na fara karatu ne da makarantar allo na fara karatun allo anan Kano, ina haɗawa da littattafai na zaure a wurin malaminmu mal Sabo nan muka yi karatun ƙawa’idi da ahalari da ashmawi da zubda da sauransu littattafai kamar nahwu. Muna zuwa makarantar dare nan ma an saka littattafai muna ɗauka. An saka ni a makarantar Firamare ta Masaƙa a shekarar 1980 har zuwa 1986.

Daga nan aka kai ni makaranta a Dutse amma ban daɗe ba Mamana ta zo ta ɗauke ni ta kai ni Kaduna gidan Sheikh Lawan Bara’u wanda a lokacin yana auren ‘yar’uwata Sayyada Nafisa ‘yar Sheikh Hassan Ciese. An saka ni a makarantar Sakandare a Kaduna mai suna Capital School daga 1987-1992. Bayan na kammala sai na shiga ABU Zaria na fara da Remedial, na yi shekara ɗaya. Daga nan sai karatuna ya tsaya na koma Senegal don neman ilimi da sauransu.

A 1999 na tafi Europe na zauna a Italy kamar tsahon shekara 10. Ina aiki da courses a ɓangarori daban-daban. Bayan na dawo Nijeriya na koma karatu inda na yi Diploma a BUK a sashen public admin sannan na yi digirina a Political Science. Ina da burin ƙara karatu. Amma ban tava aiki ƙarƙashin gwamnati ko ma wani ba duk ayyukana ayyuka ne na ƙashin kai. na nawa ne na kaina ina da ƙananan kamfanoni da kasuwancina kuma shi nake gudanarwa. Na yi kasuwanci a Kwari da kasuwanci na hannun jari da kasuwanci na oil and gas da noma sauransu.

Yaya ka fara siyasarka?

Na dawo gida daga 2011 na fsra shiga harkokin siyasa. Na shiga jam’iyyar CPC daga nan aka koma APC har na yi takara ta Majalisar Wakilai a Ƙaramar Hukumar Kumbotso. Ba mu ci takarar fitar da gwani ba a lokacin. Sai a shekarar 2019 na fito takarar gwamna a Jam’iyyar AGA. Na fara takarar an kusa zaɓe na janyewa Abba Kabir Yusuf (Abba gida-gida) lokacin yana jam’iyyar PDP.

Ya batun ƙungiyoyi?

Na shiga ƙungiyoyi da daman gaske amma dai wanda na fi mayar da hankalina akwai ƙungiyar Majma’u Ahbab ƙungiyar da take shirya taro na mauludin Shehu Ibrahim na ƙasa. Na riƙe mata national coordinator na shekara takwasa. Bayan rasuwar shugaba da mataimakinsa na zamo shugabanta ranar 24 /11/2022. Akwai kuma ƙungiyaer Ansaruldin wanda mu muka rubuta ta da hannunmu ita ma na shige ta a matsayin coordinatanta. Sai kuma Tijjaniya Grassroots Mobilization And Empowerment Initiative of Nigeria (TIGMAIN) wanda tunnain samar da ita ni ne sannan muka ƙirƙire ta kuma ni ne shugabanta na ƙasa.

Me ake nufi da Majma’u Ahbabu?

Majma’u tana nufin haɗuwa a cikin soyayyar Shehu Ibrahim Niass. Dalilin da ya sa aka sama ta suna shi ne, wurin shekara arba’in. Mutane suna haɗuwa suna yin karatu hadiyya ga maulanmu Shehu Ibrahim Niass. Akwai wanda ya zo ya gansu suna wannan karatun da yake wannan karatun ana yinsa ne duk ranar lahadi sai ya ce ai ku ne Majmau ahbab kuma ya kamata a yi mata rijista. Wannan shi ne asalin wannan ƙungiya.

Me ne aikin Majma’u?

Aikinta shi ne shirya mauludi na tunawa da haihuwar maulanmu Shehi Ibrahim Inyas, taron da babu irinsa a ƙasar nan wamda yake haɗa al’umma daga ciki da wajen ƙasar. Akwai karatun Alƙur’ani, da yi wa ƙasa addu’a wanda duk shekara ana yin sauka mai tarin yawa kuma ana yi ne don ƙaunar shehu Ibrahim. Amma muna da burin faɗaɗa wannan ayyukan nata a ƙarƙashin shugabancinmu in sha Allah.

Daga baya za mu kawo amma dai yana daga burinmu inda taron mauludin ya yi suna haka ita ma ƙungiyar sunanta ya kai. Ko’ina shi ma. Yana daga cikin manufar ƙungiyar haɗin kan jama’ar Shehu Ibrahim a ko’ina. Muna da burin abubuwan da suka shafi gina makarantu da karantarwa. Wannan jama’a da muke tarawa ya za a yi wurin karantar da ita musamman mata da samari? zawiyoyi da duk inda jama’a za su haɗu in dai za su haɗa kansu za su sami cigaba. Amma dai dole wannan ƙungiya za a sauya mata tsari sabo wanda zai kawo cigaban ƙungiyar da yardar Allah.

Me yake burge ka a rayuwa?

To, ni wallahi abin da yake burge ni shi ne na ga al’umma suna cigaba a rayuwarsu. Idan na ga mutane suna annushuwa da nishaɗi ina jin daɗi musamman almajiran Shehu Ibrahim Inyas, ina son na ga talauci yana raguwa.

Me yake ba ka haushi?

Na tsani na ga kan al’umma a rarrabe musamman Musulmi. Bare kuma in ga almajiran Shehu Ibrahim Inyas cikin saɓani. Ba na son ganin haka ina jin haushi sosai. Bana son cutar da mutane da kaskantar da su, ba na son na ga ana amfani da mutane amma su ba za su amfana ba. Ba na son na ga an yi amfani da mutum an ajiye shi a gefe. Ina jin haushin wannan abubuwa matuƙa.

Waɗanne ƙasashen ka ziyarta?

A Nijeriya kaf ba inda kafata ba ta taka ba. Kuma na shiga na yi uziri a ciki. A Afrika na je Senegal ko da yake ita gida ce, sai Nijar da Kamaru da Cadi da Mali da Burkina faso da Code’bua/Abijan da Moroko da Egypt da Epans da Spain da Belgium da Germany da Dubai da Saudia da sauransu.

Me ne burinka?

Burina nawa na kaina, to! Ina son power. Abin da yasa nake son power shi ne ƙudirina na tallafawa al’ummata. Ina son na samu abin da zan iya jagorantar mutane na yi tasiri a kansu, in ɗauki waya in ce a ɗauki wane aiki ko a taimakawa wane ko wane a yi masa kaza. Ni wannan ne burina amma ba kuɗi ba ba mulki ba ni duk wannan bai dame ni ba.

Mene ne burinka a ɗariƙar Tijjaniya?

Yanzu mu a ɗarikar Tijjaniya Alhamdlillah babu ɗariƙar da ta fi tamu a koi’ina. babu wata harka ta addini da ta kai ɗariƙar Tijjaniya a duniya amma a ɓangare guda su ‘yan Tijjaniyar wanne hali suke ciki? me ne iliminsu? me ne tattalin arziƙinsu? waɗanne irin mutane ne a ciki me ne rayuwarsu? me suke ciki wannan yana da mutuƙar muhimanci. Ni burina a yau in an zo a afara lissafa mana likitoci nawa ne da mu, baristoci nawa ne da mu, injiniyoyi da Lakcarori da masu mulki da sojoji da ‘yan sanda da malaman makaranta nawa da dai sauran ɓangarori na rayuwa.

Ina da burina a ce nawa ne jami’oinmu na Tijjaniya ? Ni maganar jami’ar nan ya dame ni, ina da wannan babban burin mu sami jami’ar Tijjaniya a ƙasar nan. Muna godewa Allah kullum kara yawa muke, amma muna kara yawa amma ina da wani buri shi ma, wannan harka ta ‘yan haƙiƙa da yake damunmu mutane su gane ba mafita ba ne a fahimta ba mafita ba ne. Yaran nan suna buƙatar ilmantarwa da nusarwa.

Me kake ganin ya ba ka ƙwarin gwiwa har ka sami wannan nasarar?

To, alhamdlillahi, ni nasan ba ni da tsoro ban taɓa tsoron wani abu ba. Kuma abin da ya ba ni wannnan kwarin gwiwar na rashin tsoron ba wani abu ba ne illa komai nawa na miƙa wa Allah ne, shi nake gani shi nake neman zaɓinsa kuma komai ya zava min ina karɓa hannu bibbiyu. Babban tsorona da fatana da burina shi ne cikawa da imani mu gama da duniya lafiya.

Me ne ya taɓa sa ka farin cikin da ba za ka manta ba?

Abin da yake saka ni farin ciki a rayuwata shi ne yadda ya ba ni iyaye masu martaba da daraja abin girmamawa a cikin al’umma. Tsatson da na fito Ina farin ciki da shi a ko da yaushe, mahaifina Shehi Sani Auwalu mahaifiyata Sayyada Aisha ‘ya ga Shehi Ibrahim Inyas. Kakana Shehi Ibrahim Niass wannan abin farin ciki ne matuƙa. Iyalaina da ’yan uwana duka ina farin ciki in na tuna su.

Muna godiya ƙwarai da ba mu lokaci.

Ni ma na gode sosai.