Babban Hafsan Tsaron Nijeriya ya jagoranci naɗa shugaban sojojin ƙasa na riƙon ƙwarya

Daga BELLO A. BABAJI

Babban Hafsan Tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa ya yi kira ga manyan sojojin ƙasa da su haɗa hannu wajen yin aiki tare da nufin kawo ƙarshen ta’addanci a Nijeriya.

Janar Musa na magana ne a lokacin da ake naɗa Manjo-Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin shugaban sojojin ƙasa na riƙon ƙwarya (COAS) a Hedikwatar Tsaro dake Abujai tare da bayyana muhimmancin aiki tare.

Manjo-Janar Oluyede zai zama jami’i na farko da aka naɗa a irin muƙamin a tarihin sojojin ƙasa na Nijeriya.

Babban Hafsan Tsaron ya ce COAS ɗin zai kasance mai cikakken iko har zuwa lokacin da Laftanal Janar Taoreed Lagbaja zai dawo daga hutun kiwon lafiya da ya tafi zuwa ƙasar waje.

Ya bayyana hakan a matsayin baƙon abu, ya na mai cewa wajibi ne a yi hakan don tabbatar da tsaro wa al’umma da ma ƙasa baki ɗaya.

A nasa jawabin, Manjo-Janar Oluyede ya miƙa godiyarsa ga Shugaba Tinubu wanda ya zaɓe shi a matsayin wanda ya dace da ɗaukar nauyin kula da ɓangaren tsaro a mataki na ƙasa.