
Daga BELLO A. BABAJI
Shugaban kamfanin yaƙi da laifukan kuɗaɗen ‘crypto’ na Binance, Tigran Gambaryan ya bayyana sunayen ƴan majalisar da suka nemi ya ba su cin-hancin Dala miliyan 150.
A watan Oktoban shekarar 2024 ne aka sako Gambaryan bayan watanni, sakamakon janye tuhumar badaƙalar kuɗaɗe da Gwamnatin Tarayya ta shigar akan kamfaninsa, wanda hakan ya biyo bayan shiga tsakani da Gwamnatin Amurka ta yi.
A lokacin da aka tsare shi, Gambaryan ya ce akwai wasu ƴan majalisa da suka buƙaci ya ba su cin-hanci don ya kuɓuta daga kamawa ko maka shi a kotu.
A wani rubutu da ya wallafa a shafin X, Gambaryan ya ce ƴan majalisar sune; Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Philip Agbese; Ginger Obinna Onwusibe, Shugaban kwamitin yaƙi da rashawa na Majalisar Wakilai; da ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Obanliku/Obudu/Bekwara, Peter Akpanke.
Ya kuma ce DSS tana cikin batun tare da Majalisar Wakilan, waɗanda sun gana a ranar 5 ga watan Junairun 2024 don tattauna batun.
A lokacin zaman ne aka samu wasu kamarorin bogi da ko kunna su ba a yi ba, inda a nan ƴan majalisar suka nemi da ya ba su cin-hancin daga kuɗaɗen ‘crypto’ zuwa asusunsu na kai-da-kai.
Saidai, zuwa lokacin haɗa rahoton, ba a samu wani batu daga kowane ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin su da batun karɓar cin-hancin ba.