Babban likitan Falasɗinu ya rasu a kurkukun Isra’ila

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ƙungiyoyin masu kula da fursunonin Falasɗinu sun ce wani babban likita Bafalasɗine ya mutu a gidan yarin Isra’ila bayan shafe sama da watanni huɗu yana tsare.

Dr Adnan Al-Bursh, mai shekaru 50, shi ne shugaban likitoci a asibitin al-Shifa.

Ma’aikatar gidan yarin Isra’ila ta tabbatar da cewa wata sanarwa da aka buga a ranar 19 ga Afrilu game da wani fursuna da aka tsare saboda dalilan tsaron ƙasa ya mutu a gidan yarin Ofer shine Dr Al-Bursh.

Ba a bayar da cikakken bayani kan musabbabin mutuwar ba, kuma hukumar gidan yarin ta ce ana binciken lamarin.

Sai dai ƙungiyoyin fafutukar kare haƙƙin Falasɗinu a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da suka fitar a ranar Alhamis sun ce mutuwar Dr Al-Bursh “kisa ce” kuma har yanzu gawarsa tana hannun Isra’ila.

Dr Al-Bursh shi ne shugaban likitoci a cibiyar kiwon lafiya mafi girma a Gaza, asibitin al-Shifa, wanda sojojin Isra’ila suka kai farmaki sau da dama.

Yana aiki na wucin gadi a asibitin Al-Awada da ke arewacin Gaza lokacin da sojojin Isra’ila suka tsare shi.

Abokan aikinsa sun karrama marigayi likitan tiyatar, inda suka bayyana shi a matsayin “mai tausayi” da kuma “jarumi”.

Daraktan Al-Shifa, Dr Marwan Abu Saada, ya ce labarin rasuwarsa abu ne mai ƙona rai.

Wani abokin aikinsa, Dokta Suhail Matar, ya kira Dr Al-Bursh “ma’abocin aminci” ga kowane sashen kiwon lafiya a duk asibitocin Gaza.