Daga CRI HAUSA
A ranar 15 ga watan Fabrairun 2022, jaridar Leadership ta Nijeriya ta wallafa wani sharhi da sanannen mai sharhi na Nijeriya Ray Morphy, ya rubuta, mai taken, “Ƙasar Sin darasi ne da ya kamata Nijeriya ta yi koyi”, inda ya bayyana cewa, ƙasar Sin ta yi nasarar fita daga ƙangin talauci da koma bayan ci gaba a cikin wasu gwamman shekaru ‘yan kaɗan. A cikin ƙanƙanin lokaci Sin ta cimma gagaruman nasarori na ban mamaki. Nasarorin da ƙasar Sin ta samu ya nuna cewa, muddin shugabanni suna da burika masu tasiri, tabbas ne za a samu gagarumin canji.
Nasarorin da ƙasar Sin ta cimma a shirinta na kawar da talauci ya ƙara ilmantar da bil adama game da yaƙi da talauci, ya zama tamkar wani salon abin koyi ga duniya a yaƙi da talauci, kuma ya ƙara wa dukkan ƙasashen duniya ƙaimi, musamman ƙasashe masu tasowa, game da shirin yaƙi da talauci.