Babban taron APC: An tantance Sanata Abdullahi Adamu da sauran ‘yan takara

Daga BASHIR ISAH

Akwai yiwuwar kwamitin tantance ‘yan takara da babban kwamitin APC ya kafa ya tsawaita aikinsa gaba da Laraba.

Bincike ya nuna an samu saɓanin lokacin da aka tsayar wa tawagar Gwamna Aminu Masari na Katsina don tantance su a matsayin masu neman muƙamin kwmitin gudanarwa na uwar jam’iyya (NWC), wanda hakan ya sanya kwamitin bai kai ga kammala tantance masu neman muƙaman ciyaman da sakatare a Talata ba.

Tun farko, sanarwar da sakataren kwamitin tantancewar, Emmanuel Otagburuagu ya sanya wa hannu ta nuna za a tantance masu neman kujerar ciyaman da sauran muƙaman NWC ne a ranar Talata, yayin da aka shirya tantance masu neman muƙamai na shiyyoyi a ranar Laraba.

Sai dai bincike Blueprint Manhaja ya gano cewa ya zuwa Talatar da ta gabata kwmaitin ya gaza kammala tantance baki ɗayan waɗanda aka shirya tantance a wannan rana.

Bayanai sun nuna a jiya Laraba ɗan takarar shugaban jam’iyya, Sanata Abdullahi Adamu da sauransu masu neman muƙamai a NWC sun haɗu da ‘yan takarar muƙamai na shiyyoyi a masaukin baƙi na gwamnan Katsina da ke Asokoro, Abuja don a tantance su.

An ga Sanata Abdullahi Adamu ya isa wajen tantancewar da rana inda ya tafi ya cimma kwamitin don a tantance shi.

Daga cikin waɗanda aka samu tantancewa ran Talata da daddare har da tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Osun, Sanata Iyiola Omisore da Sanata Sani Musa da Tanko Al-Makura da George Akume da kuma Saliu Mustapha.

Ya zuwa haɗa wnannan labari, shirin tantance ‘yan takarar muƙaman shiyyoyi ya ci gaba da gudana a ran Laraba.