Babban titin da Sin ta gina zai bunƙasa ɓangaren yawon buɗe ido a Kenya

Daga CMG HAUSA

Ana sa ran babban titin da ƙasar Sin ta gina a ƙasar Kenya, zai bunƙasa ɓangaren yawon bude ido na ƙasar.
Sakataren ma’aikatar kula da yawon buɗe ido da namun daji na ƙasar, Najib Balala ne ya sanar da hakan ga manema labarai a birnin Nairobi, babban birnin ƙasar, yana mai cewa, ana sa ran motoci za su fara gwada titin daga ran Asabar.

Ya ƙara da cewa, wannan wata makoma ce mai haske ga ɓangaren yawon buɗe ido na kasar, saboda ana sa ran babban titin na Nairobi zai rage lokacin da ake ɗauka daga filin jirgin sama zuwa wuraren yawon buɗe ido daban-daban dake faɗin ƙasar.

Ya ci gaba da cewa, sun lura masu yawon shakatawa na fuskantar jinkirin tafiya tsakanin filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Jomo Kenyatta da cibiyar hada-hadar kasuwanci ta birnin. Amma da wannan babban titi, minti goma kacal ababen hawa za su ɗauka daga bangaren masu sauka a filin jirgin, zuwa cibiyar birnin, maimakon sama da sa’o’i 2 da suke ɗauka a yanzu.

Ƙarƙashin wani haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanin gine-gine na China Road and Bridge Corporation ne aka samar da kudin ginin babban titin mai tsawon kilomita 27.1 da ya hada da hannu biyu da kuma hannu 6.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha