Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Dr. Bello Mohammed Matawalle ya amince tare da fitar da Naira miliyan 200 na saye da raba shanu da raguna da kuma tsabar kuɗi ga al’umma daban-daban a jihar don gunar da bikin Babbar Sallah da ke tafe.
Sakataren yaɗa labarai na Jam’iyyar APC na jihar, Yusuf Idris ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya miƙa wa Blueprint Manhaja ranar Asabar.
Matawalle, wanda shi ne Jagoran jam’iyyar APC a jihar, ya umarci shugabannin jam’iyyar APC na jihar a ƙarƙashin shugabanta, Hon. Tukur Umar Danfulani, da ya jagoranci rabon kayan domin duk waɗanda aka yi domin su saƙon ya isa gare su.
“A ƙarƙashin wannan tsari, ‘yan jam’iyyar APC da magoya bayanta, ƙungiyoyin mata da matasa da kuma wasu zaɓaɓɓun mutane a faɗin jihar za su samu kasonsu bisa adalci,” in ji Yusuf.
Ya ƙara da cewa, “Sauran waɗanda za su amfana da tallafin sun had’ɗa da marayu da marasa galihu da magoya bayan jam’iyya da malaman addinin Musulunci da masu aikin yaɗa labarai da masu gudanar da shafukan sada zumunta da dai sauransu.”
Hakazalika, Hon. Tukur Ɗanfulani, wanda ya miƙa godiyarsa ga tsohon Gwamna Bello Mohammed Matawallen Maradun bisa wannan karimcin, ya ce tallafin yana zuwa a daidai lokacin da ya yi nuni da cewar karamcin zai taimaka wajen rage ƙuncin rayuwa a tsakanin al’umma .
Tuni Ɗanfulani ya ce an kafa kwamitin da zai tabbatar da cewa duk waɗanda aka zayyana sun samu nasu kason.
Ya kuma buƙaci sauran al’umma da su yi koyi da tsohon Gwamnan a kan wannan yunƙuri wanda gagarumin fa’idar yin haka zai same su duniya da lahira.
Matawalle ya kuma bukaci al’ummar musulmin jihar da ma ƙasar nan da su ƙara zage damtse wajen gudanar da ibada a kwanaki goma na farkon Zul-hajji domin neman taimakon Allah domin kawo ƙarshen matsalolin tsaro da ke addabar Zamfara da sauran sassan ƙasar nan.
Ya nemi addu’o’i na musamman domin samun nasarar aiwatar da sabon tsarin ciyar da ƙasar nan gaba na Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya ƙaddamar domin amfanin ‘yan Nijeriya.
Blueprint Manhaja ta tattaro cewa mambobin kwamitin sun haɗa da Sakataren jam’iyyar APC na jihar, Hon. Ibrahim Umar Ɗangaladima, Mallam Yusuf Idris Gusau, Dr. Nura Isah, Dr. Jalaludeen Ibrahim Maradun, Surajo Habib Tsafe, Hon. Yusuf Abubakar Zugu da Hon. Ibrahim Maaji.