Babu abin da ya fi kasuwanci daɗi a wannan zamani – Dije Abdulƙadir

“Dole sai matasa sun cire girman kai da raina ƙaramar sana’a za a samu cigaba”

Daga ABUBAKAR M TAHEER a Haɗejia

Mai karatu, wannan tattaunawa ce ta musamman da Hajiya Dije Abdulƙadir, wacce ’yar kasuwa ce kuma mai fafutukar wayar da kan mata muhimmanci neman na kansu. A cikin zantawar, ta kawo yadda ta fara kasuwanci da ƙaramin jari har ta zama babbar ‘yar kasuwa wadda take sana’arta a yanzu ta hanyar yanar gizo da dai sauran bayanai. A sha karatu lafiya:

MANHAJA: za mu so ki gabatar da kanki ga masu karatu.
DIJE ABDULƘADIR: Assalamu alaikum warahamatullahi wa baraka tuhu. Sunana Dije Abdulƙadir. An haife ni a Jihar Filato a shekara ta 1970, wanda ya kama shekaru 51 yanzu. Na yi karatun firamare har zuwa aji biyar. Da ya ke babana ma’aikaci ne an yi masa ‘transfer’ zuwa Kano sai mu ka dawo Kano inda na ci gaba da karatu a shekarar ƙarshe ta firamare, inda na gama na samu damar tafiya makarantar ‘yan mata ta Dala, wato GGC Dala. Daga nan aka min aure har na samu ‘ya’ya uku.

Na samu damar ci gaba da karatu, inda na kammala NCE har ma na samu aikin koyarwa, ba jimawa na samu wani aikin a asibitin Malam Aminu Kano ɓangaren ‘Accountancy’.
Bayan fara aiki da shekara ɗaya sai ya zama an yi ma maigidana ‘transfer’ zuwa Sakkwato, hakan ya sa dole na ajiye aikin.

Yaushe ne kika shiga kasuwanci gadan-gadan?
Bayan mun koma Sakkwaton ne na fara tunanin abin yi, sai tunanina ya tafi ga kasuwanci. Wannan ta sa na yi aike kasuwar Kwari aka siyo min kayan sanyawa, shadda da leshi. A lokacin guda asirin-ashirin kawai na siyo. Sai dai abin mamaki, ana kawo su ba ɓata lokaci suka ƙare. Don haka ba vata lokaci na sake turawa aka kawo min wasu. A gaskiya a lokacin na yi mamakin irin ribar da na samu cikin ƙanƙanen lokaci.

A take na fahimci irin alfanun da ke cikin irin wannan sana’a, don haka sai na dage. Har na kai ga buɗe shagon ɗinki, ana ɗinkawa, mu na siyar da har ɗinkakku. Ta kai har wasu garuruwan za mu kai. Bayan na fuskanci alkairin da ke cikin wannan sana’a, sai na fara tunanin yadda zan faɗaɗa ta, wannan ta sa na shiga harka saida kayan ‘Kitchen’ na mata wanda na ke safararsu daga Chana, Turkiyya da Dubai.

Ta ya kike haɗa zamantakewar aure da kasuwancinki, ganin cewa ki na fita har wasu ƙasashen siyo kaya?
To a gaskiya wannan ya samo asali ne daga ɓangaren mijina, wanda yake babban ma’aikaci kuma manomi. Wannan ta sa ba ni samun wata tangarɗa. Haka kuma da yake ina da yara kusan guda takwas, waɗanda dukkansu suna makaranta, wasu sun kammala, sun samu aiki, to ka ga babu wahala kula da yara za a ce.

Da yake ababe da dama sun canza saboda canjin da zamani ya zo da shi, ciki kuwa har da kasuwanci. Shin ta yaya kike gudanar da kasuwanci a yanzu?
Da yake ina da shago a Kano, wannan ta sa duk mai son kayana ya kan je shago ya siya. Haka kuma a yanzu da yake muna wata rayuwa ta cigaba kamar yadda ka ce, na kan ɗora a shafina na ‘Facebook’ ko ‘Instagram’ ko kuma a ‘WhatsApp Status’ ɗina wanda duk yake so ya kan iya lalubata, ni kuwa sai in aika masa da kayan a duk inda yake a faɗin ƙasar nan. Ka ga sauƙi ya samu kenan.
 
Komai na rayuwa ba ya rabuwa da ƙalubale. waɗanne ƙalubale kika fuskanta a sana’arki?
Wannan gaskiya ne. Eh a gaskiya ƙalubalen bai wuce na harka da mutane ba, inda za ka aikawa mutum kaya, amma a ƙarshe a zo ana jinku da shi.

Wane irin ƙoƙari kike domin wayar da kan mata ‘yan’uwanki wajen yin kasuwanci na zamani?
Eh, haƙiƙa yanzu na fara tunani kala-kala kan yadda zai zama mun faɗakar da mata muhimmancin kasuwanci ta zamani musamman mata da suke a gida kullum da kullum babu abin yi in banda chat. Kuma ko kwanan nan mun je Ƙasar Benin kan irin tunananin farkar da mata da matasa muhimmancin neman na kansu.Wanda kwanan nan za a ƙaddamar da shirin tallafawa matasa da mata dabarun kasuwanci. A yanzu haka na fara shirin buɗe gidauniya ta wa ta kaina wanda kuma maƙasudinta shi ne, wayar da kan mata na birni da na karkara.

Wane kira kike da shi ga mata ‘yan’uwanki?
To a gaskiya kiran da na ke da shi gare su shi ne, duk abinda za ka samu a rayuwa ba ya samuwa ta hanyar sauƙi, sai an sha wahala. Kar ki ce ba ki da jari don haka ba za ki yi sana’a ba. Yanzu duniyar ta canza, sauƙi ya samu ta fuskar kasuwanci. ko ba ki da sisi za ki iya siya, ki saida a kafafen sada zumunta. Za ki iya fara kasuwa a ‘zero Kobo’. ma’ana ba ki da ko sisi. Ta ya hakan za ta kasance; idan wata ta ɗora kayan siyarwanta, sai ki mata magana za ki dinga ɗorawa a shafinki, da zarar wasu sun gani shikenan ki mata magana, ta ba ki farashi ke ma ki samu riba ki na ragewa. Musamman idan mutum ya riƙe gaskiya zai samu riba mai tarin yawa ta wannan hanya. Yanzu abinda ake yi kenan. Kuma wannan tsohuwar al’adar iyayenmu da kakannin mu ce ta dillanci indai mutum ya saka tsoron Allah yanzu ne shima zai samu jari na sa na ƙashin kansa. Haka matan da aka mutu aka bar musu ‘ya’ya su rinƙa sana’a komin ƙanƙantarta domin su samu abinda za su ciyar da marayu.

Wani kira kike da shi ga matasa musamman waɗanda suka kammala karatu suke jiran gwamnati ta ba su aikin yi?
To, maganar gaskiya kiran da na ke da shi ga yaranmu masu tasowa musamman maza, kai har matan, waɗanda suka kammala karatu shi ne; a yanzu gwamnati ba ta da guraben aikin da za ta bayar saboda an cika harma an batse kuma ita ma tana fama da matsalar ƙarancin kuɗi. Kuma maganar gaskiya, matasanmu yawancin su zuciyarsu ta mutu, so suke a ce cikin ƙanƙanin lokaci sun samu kuɗi.

Shi kuma kuɗi ba ya samuwa haka kawai sai an dage an yi aiki tuquru. Duk wanda ka ga ya samu komai na rayuwa sai da ya jajurce ya kuma dake nasara ba ta samuwa lokaci guda sai a hankali. Kuma dole sai sun cire girman kai da raina sana’a komai ƙanƙantarta. Misali a ƙasashen da suka ci gaba za ka ga babban ma’aikaci bayan tashi daga aiki ya fito yana ‘taɗi’ da motarsa don samun na cefane a gidansa. Ka ga albashi na sa an rage masa nauyi. Ko a nan Benin na haɗu da wani ‘Graduate’ wanda ya kammala karatu sama da shekara goma bai samu aiki ba, wannan ta sa ya siyar da gonar gadonsu yake tuqin tasi.

Waɗanne nasarori za a ce kin samu a harkar kasuwa?
To haƙiƙa na samu dubban nasarori, na je ƙasashen duniya da dama, na je na sauke farali a Saudiyya. Kuma hatta wasu ma ta hanyar kasuwancinmu sun samu rufin asiri.

Menene babban burinki a kasuwanci?
Babban burin da na ke da shi a harkar kasuwanci na zama kamar Ɗangote ko kuma na wuce shi.

Mun gode.
Ni ma na gode ƙwarai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *