Bincike: Babu abin da za ku nema ku rasa, cewar INEC ga jam’iyyar LP

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta ce a shirye take ta ba da damar bincikar bayanan zaɓen da ya gudana ran 25 ga Fabrairu ga duk jam’iyyar da ke da buƙatar hakan.

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar lauyoyin Jam’iyyar Labour ƙarƙashin jagorancin Dr Livy Uzoukwu, SAN, ranar Litinin a Abuja.

Da yake jawabi, Yakubu ya faɗa wa lauyoyin cewa ya samu sanarwar zuwansu ta wasiƙar da aka aiko masa mai ɗauke da kwanan wata 6 ga Maris, don bincikar kayayyakin da aka yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen.

Kazalika, ya ce wasiƙar ta kuma buƙaci a sanar da kwamishinonin zaɓe na jihohi 36 har da Abuja, cewa kowa ya sahale bayanan da ke wurinsa don bincike sakamakon ƙarar da Jam’iyyar LP ta shigar kotu.

Yakubu ya ce INEC ta yi zama da duka kwamishinonin domin duba yadda za ta ba da sahihin kwafin bayanan ayyukan zaɓen ga jam’iyyun da suka buƙaci hakan.

“Ina mai tabbatar muku babu wani bayani da hukumar za ta ɓoye ma kowa, kuma za ta samar da duka bayan da aka nema.

“Ku sani babu wani abu da INEC za ta ɓoye, duk abin da kuka nema za a ba ku shi,” in ji Yakubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *