Babu alamar kasafin kuɗin 2025 zai taimaki talaka

Assalamu alaikum, Blueprint Manhaja. Haƙiƙa mun yi farin ciki da sake ba mu dama wurin bayyana abubuwan da suke mana kaikayi a rai tare da isar da saƙon da muke son isarwa ga shugabanni da sauran al’ummar ƙasa. Muna muku addu’ar Allah ya ƙara muku hikima da basirar aiki da kuma bunƙasar wannan jarida mai farin jini baki ɗaya.

Abin kunya ne kwarai da gaske a irin halin da wannan ƙasa tamu da ma al’umma musamman ma’aikata ke rayuwa cikin ƙunci a ce shugaba Tinubu ya ware wasu kuɗaɗe domin amfanin kansa da kansa, wanda kuɗin abincinsa kaɗai na rana guda ya kai albashin sama da mutum biyar.

Inda idan aka kasafta kuɗin abincinsa na rana ɗaya izuwa gida biyar, za su kama naira dubu hamsin da uku da ɗari takwas da sittin da uku (N53,863). Wanda wannan abin kunya ne kwarai da gaske a ƙasar da Naira 100,000 ke neman gagara a matsayin mafi ƙarancin albashi, a kuma ƙasar da albashin ma da ƙyar ake iya biya.

Sannan a ce an ware sama da miliyan arba’in domin sayen ruwa da lemu, wanda kuɗinnan baki ɗaya za su zarare ne a tsakanin shugaban ƙasa da mataimakinsa.

Babu shakka wannan kasafin kuɗi ba a yi domin talaka ya amfana ba, sannan duniya za ta kalli shugaban da ake cewa mai adalci a matsayin marar tausayi idan aka yi duba da irin halin ƙunci da talauci da talaka ke fuskanta a halin su kuma a ƙarƙashin mulkin shugaba Bola Tinubu.

Lokaci ya yi da ’yan Nijeriya za su fahimci cewa, shugaba Bola Tinubu ba fa talakawa ba ne a gabansa. Domin ya bi duk inda talaka zai amfana da shi ya rage kuɗin, sannan ya ƙara wa wurare marasa amfani kuɗaɗe masu yawan gaske. Gaskiya mu dai talakawa sai dai mu koma ga Allah, sannan mu ci gaba da addu’a a kan Allah ya kawo mana sauƙin rayuwa.

Wassalam. Wasiƙa daga MUHAMMAD AWWAL (Ya Muha), 08062327373.