Babu barazanar tsaro ga zaɓen 2023 — Sufeto-Janar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Sufeto-Janar na ‘yan sandan Nijeriya, Usman Alkali Baba, ya tabbatar da cewa babu wata barazana ga gudanar da zaɓen 2023.

Sufeto-Janar ya bayar da wannan tabbaci ne a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Lahadi a Abuja.

A cewar Baba, wannan tabbacin ya biyo bayan nazarin barazanar tsaro da ‘yan sanda su ka yi, ta yin amfani da mafi kyawun tsari a duniya don tabbatar da yanayin da ake sa ran za a gudanar da zaɓen.

Baba ya yi magana ne a wata ganawa da Todd Robinson, mataimakin sakatare, ofishin kula da harkokin miyagun ƙwayoyi da tabbatar da doka da oda, ma’aikatar harkokin wajen Amurka.

Sufeton ya gana da jami’in ne a yayin taron shugabannin ‘yan sandan Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda aka gudanar a Amurka.

Ya ce batutuwan da a ka tattaunawa a wurin taron sun ta’allaƙa ne kan inganta tallafin da ake bai wa shirin horas da ‘yan sandan Nijeriya.

Baba ya ce an fi mayar da hankali ne musamman kan horar da rundunonin dabarun yaƙi da aka tura a yankin Arewa maso Gabas da sauran yankunan da ta’addanci ya yi ƙamari a ƙasar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *