Babu buƙatar tada hankula game da rigakafin korona – Gwamnati

Daga UMAR M. GOMBE

Gwamnatin Tarayya ta hori ‘yan Nijeriya da su kwantar da hankulansu dangane da rukunin rigakafin korona na Oxford-AstraZeneca da ta karɓa saboda a cewarta, babu wata illa a tattare da rigakafin.

Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko (NPHCDA) ita ce ta bada wannan tabbaci a wata sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis ta hannun shugaban sashenta na hulɗa da jama’a, Mohammad Ohitoto.

Yayin da wasu rahotanni ke nuni da wasu ƙasashe sun dakatar da yin allurar, amma hukumar NPHCDA ta buƙaci ‘yan Nijeriya kada su tada hankulansu.

Hukumar ta ce yayin da take lura da damuwar da aka nuna game da wani takamaiman rukuni na maganin AstraZeneca, wato ABV5300, ta ce ana kan gudanar da bincike don sanin ko rukunin ya kasance ta kowace hanyar da ke da alaƙa da tasirin sakamako.

Hukumar ta jaddada cewa Nijeriya ba ta karɓi magani ba daga rukunin da aka ɗora wa alamar tambaya. Ta ce abin da ake ganin matsala ce daga rigakafin da Nijeriya ta samu tuni an magance shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *