‘Babu hannu Gumi a lamarin ceto ɗaliban Kuriga’ — Gwamna Sani

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa babu hannun malamin nan na Islama, wato Sheikh Ahmad Gumi a lamarin ceto ɗaliban firamaren da aka yi.

Uba Sani ya faɗi hakan ne a wani shirin da Tashar Channels Television ta yi da shi a ranar Lahadi.

Yana mai cewa, sojoji ne suka ceto yara 137 da aka kuɓutar da su bayan da ‘yan bindiga suna yi garkuwa da su a ranar 7 ga Maris a yankin Ƙaramar Hukumar Chikun a jihar.

Ya ƙara da cewa, an kuɓutar da yaran ne inda aka kai su aka ɓoye a wani yanki na Jihar Zamfara.

Sani ya ce ji-ta-ji-ta cewa kawai ake yaɗa cewa da ake yi an biya kuɗin fansa wajen kuɓutar da yaran, tare kuma da jaddada cewa babu hannun Sheikh Gumi cikin lamarin ceto ɗaliban.

Haka nan, ya ce saɓanin rahoton da aka yaɗa, yaran da aka kuɓutar ɗin su 137 amma ba 287 kamar yadda aka yaɗa. Ya ce yaran sun ƙunshi ɗaliban firamare da na sakandare da aka yi garkuwa da su a yankin Kuriga kimanin makonni huɗu da suka gabata.