Babu inda muka umarci a zaɓi PDP a kujerar Shugaban Ƙasa a Katsina – Lawal Boye

Daga RABIU SANUSI

Rahotanni daga jihar Katsina na bayyana cewa Shugaban Jamiyyar Accord a Jihar Katsina, Salihu Lawal Boye, ya musanta rahotonnin dake cewa Jamiyyar ta goyi bayan ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jamiyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaɓen da ya gudana Asabar.

Salihu Lawal Boye ya bayyana haka ne alokacin zantawa da manema labarai a Katsina.

Ya ce ɗan takarar Gwamnan Jihar Katsina a Jamiyyar Accord wanda ya goyi bayan Alhaji Atiku Abubakar yayi haka ne bada yawun uwar Jamiyyar ba.

Yayi kira ga ɗimbin magoya bayan Jamiyyar da su yi watsi da maganganun ɗan takarar Gwamnan Jamiyyar ta Accord wanda ya yi haka ne don son kansa ba don Jamiyyar ba.

A jawabansu daban-daban, shugabannin jamiyyar a shiyyoyi Uku na Jihar Katsina Abubakar Ismail da Aminu Maska da Mustapha Lawal sun ce Jamiyyar ba ta goyi bayan kowane ɗan takarar Shugaban Ƙasa ba.