Babu laifin mu a wahalar man fetur da a ke yi a Nijeriya – IPMAN

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ƙungiyar Dillalan Man fetur ta Ƙasa, IPMAN, ta fitar ce ba laifinta ba ne a ƙarancin man fetur da ake fama da shi a ƙasar.

Ƙungiyar ta kuma ce mambobinta ba su da hannu a ƙarancin da ake fama da shi a halin yanzu.

Femi Adelaja, Shugaban IPMAN ta defot ɗin Mosinmi a Jihar Ogun, a wata sanarwa da ya fitar a ƙarshen mako, ya ce babu man fetur a cikin gidajen man fetur na ƙasa (NNPC) a faɗin Nijeriya.

Ya ce a yanzu haka farashin man fetur daga defot ya kai Naira 220 a faɗin gidajen man da ke Legas.

A cewarsa, ‘yan kasuwan sun koma siyan kayan ne daga defot-defot na masu zaman kansu, inda suke sayar da kayan a farashi mai tsada.

Don haka ya danganta matsalar ƙarancin man da ake fama da ita a halin yanzu ga gwamnatin tarayya da kuma gazawar kamfanin man fetur na ƙasa (NNPC) wajen samar da man ga mambobinsa a farashi mai sauƙi.