Babu wanda ya taimaka wa Shugaba Buhari yayin da aka rufe kan iyakokin ƙasa – Uba Yakasai

Daga BABANGIDA S. GORA a Kano

Dangane da buɗe iyakokin ƙasa da Gwamnatin Tarayya ta yi kwanakin baya, Alhaji Uba Zubairu Yakaisa, wanda shi ne shugaban kasuwannin Sabongari, Singa da Galadima da ke Kano, ya bayyana cewa babu wanda ya taimaka wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari don ganin an samu gagarumar nasarar kulle iyakokin, musamman wajen bunƙasa harkar noma.

Yakasai ya kuma bayyana cewa, “ba batun ɓoye-ɓoye manyan ‘yan kasuwar da suke iƙirarin cewa za su taimaki Maigirma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yayin rufe waɗannan iyakoki lokacin baya ba su ba shi goyon baya ba wajen abinda suka ɗauka a matsayin alƙawarin taimakon kawo cigaba ga manoma da noman a ƙasar nan.’

Shugaban ya kuma ƙara da cewa lallai sun yi zaton gwamnati za ta buɗe wannan iyakoki tun a baya ba sai an kawo yanzu ba, domin a cewarsa da yawan ‘yan kasuwar da ke da damar kawo tirela goma a baya, yanzu ba su da damar kawo tirela uku, don sun karye ba su da qarfin arziki kamar baya, inji shi.

Yakasai ya kuma tabbatar da tarin shinkafar da Gwamnatin Tarayya ta nuna wata biyu baya amma kuma har yanzu babu ɗan kasuwar da ya fito ya yi godiya akan abinda gwamnati ta yi mashi kuma babu wani labari akan wannan dalar shinkafa da aka nuna.

Sannan ya ce lallai wasu manyan ‘yan kasuwa da masu kamfanoni na da hannu wajen taimakon ƙaƙaba wa talakawa matsi da tasgaro a wannan hali da aka tsinci kai a halin yanzu na matsin rayuwa da ake ciki.

Kazalika ya bada misali da manyan ‘yankasuwa na baya da suka bada kansu tare da taimakon na ƙasa, kamar Marigayi Isiyaka Rabiu, Alhaji Aminu Ɗantata da har yanzu yana da rai suna matuqar taimkon ƙananan ‘yan kasuwa da sauran jama’a.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *