Daga BELLO A. BABAJI
A ranar Laraba ne Hedikwatar Tsaron Nijeriya, DHQ ta ƙaryata wani rahoto da aka jingina wa Majalisar Dokokin Jihar Neja da ke cewa sansanin horon sojoji na ƙaramar hukumar Kwantagora na ƙarƙashin ikon ƴan bindiga.
Blueprint ta ruwaito cewa Majalisar ta tattauna wani batu da ke roƙon Gwamna Mohammed Umar Bago ya haɗe kai da sojoji wajen tabbatar da kora ƴan bindiga daga babban sansanin horo na sojoji dake ƙaramar hukumar.
Saidai, Rundunar sojojin ta ofishin Daraktan Labaranta, Manjo-Janar Edward Buba, ta ce zargin bai tabbata ba, inda an samu ba-takashi ne a tsakanin sojoji da ƴan bindigar, amma babu wani yanki na ƙaramar hukumar dake ƙarƙashin ƴan ta’addar.
Daraktan ya kuma ce, sojoji na aiki kafaɗa-da-kafaɗa da gwamnatin jihar don inganta tsaro wa al’ummar jihar.