Babu wata aniyar ƙara kuɗin fetur, cewar NNPC

Daga FATUHU MUSTAPHA

Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPC) ya jaddada cewa ba shi da wata aniya ta ƙara kuɗin mai nan kusa.

Shugaban kamfanin, Mele Kyari, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya bayar.

Kyari ya bada sanarwar haka ne yayin ganawar da ya yi da manema labarai jim kaɗan bayan tattaunawar sirri da suka yi tare da Ƙungiyar Masu Motocin Haya ta Ƙasa (NARTO) da takwararta ta direbobi masu dakon mai (PTD), Litinin da ta gabata a Anuja.

NNPC ya nemi ganawa da ƙungiyoyin ne bayan da mambobin PTD suka bai wa NARTO wa’adin mako guda kan ta magance matsalar ƙarin albashin mambobinsu ko kuma su tsunduma yajin aiki.

Albarkacin ganawar da NNPC ya yi da su ya sa direbobin suka janye barazanar shiga yajin aikin da suka yi, tare da alƙawarin komawa bakin aiki.

Kyari ya buƙaci ƙungiyar da ta hanzarta yin abin da ya dace domin hana aukuwar matsalar ƙarancin mai a gidajen mai a faɗin ƙasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *