Bacci a jikin ɗan adam (2)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu, Assalamu alaikum. Barkan mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi da ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Idan kun shirya, bismillah!

A makon da ya gabata,  na fara bayani ne a kan yadda bacci ya ke a jikin ɗan adam. Inda na fara somin tavin manyan al’amura da sula shafi bacci. Na faɗa cewa bacci maudu’i ne mai faɗin gaske, wanda ya ke da alaƙa da rayuwar ɗan adam ta fuskoki da dama irinsu: nutusuwa, hankali, ganewa, azanci, fahimta, saiti, da sauransu. Haka kuma yana da alaƙa da lafiyar gaɓɓan jiki irinsu zuciya, ƙwaƙwalwa, kayan ciki, jini, da sauran gaɓɓai. 

Sannan idan ba a manta ba, na faɗi cewa manyan ƙasashe da su ka cigaba sun samu masana da suka dukufa ka’in-da-na’in wajen binciko sirrikan da ke ɗamfare fa bacci da rawar da yake takawa a jiki, da kuma illolin da ƙaracinsa ko rashinsa ke haifarwa a jikin ɗan Adam.  Akwai wata gidauniya mai suna “Sleep Foundation” a birnin Washington da ke ƙasar Amurka. Aikin wannan gidauniya shi ne ilmintarwa da wayar da kan jama’a, da bada shawarwari game da bacci, da bincike akan yadda za a inganta shi. 

Inyi muku tuni, shi bacci a ɗabi’ance, yana riskar ɗan Adam ne bayan da shi ɗan Adam ɗin ya gama gudanar da ayyuka yini na wannan Rana, to a ƙarshen yinin, jikinsa ko jikinta ya gaji, ba kuma abinda yake buƙata illa bacci. Kamar yadda na faɗa, bacci ne ke hutar da jikin ɗan Adam daga gajiyar wuni cikin hidimomi na wannan rana. Na bada bayanin me ke faruwa idan bacci ya zo wa mutum, har ma na kawo labarin wani masanin ƙwaƙwalwa da tunanin ɗan Adam mai suna Matthew Walker. 

Ma’anar bacci kuwa, zan iya cewa shi bacci wani yanayi ne wanda jiki da ruhin ɗan Adam su ke shiga domin hutawar jikin da ruhin daga gajiyar da ta yi ɗawainiya da shi (ruhin da hangar jikin) tsawon wannan wuni. Bacci yana faruwa ne kowacce rana, inda a ɗabi’ance, ya fi faruwa yayin da wuni ya ƙare, dare ya shiga. Malam bahaushe ya na cewa:”dare mahutar bawa.”

Bacci yana da yanayi. Wannan shi ne halin da za a samu mutum yayin da bacci ya zo masa. Idan ɗan adam zai shiga yanayin bacci,  zai rufe idanunsa ko idanunta, gaɓɓan jikinsa za su shika, tsokar nama ta sassan jikinsa za su sakata (musamman masu motsawa yayin gabatar da manyan al’amura irinsu tafiya, gudu, magana, da sauransu), wartsakewarsa za ta gushe. Shi yasa idan ɗan adam ya na bacci, to fa a tsakiya yake: tsakanin rayuwa da mutuwa; tsakanin mai hankali da marar hankali; tsakanin zahiri da gaibu. 

A lokacin da mutum ke wannan yanayi, bai San me ke wakana ba! Kuma dukkanin sassan karɓar saƙo na musamman irin su ji, gani, magana, ɗanɗano, jin ƙamshi ko wari, sun shiga khusufi. Lallai bacci yayi kama da nutsuwa amma numfashi ya hana! Bacci yana da nau’i guda 2: mai nauyi da kuma mai sauƙi. Na yi bayanin yadda kowanne yake a rubutun da ya wuce. Haka kuma bacci ya na da matakai guda huɗu. Na yi cikakken bayanin matakan a rubutun satin da ya wuce. Na faɗa cewa matakan su na maimaita kansu ne har izuwa lokacin da Allah ya nufin mutum da farkawa. 

Mataki na ƙarshe shi ne wanda a cikinsa idanu za su dinga mommotsawa da sauri (REMs) Gudun jini a magudanansa zai fara ƙaruwa; zuciya za ta ɗan fara bugawa da sauri fiye da daa, shima numfashi zai ɗan ƙara sauri. Wannan mataki ya kan fara ne yayin da mutum ya samu kimanin awa ɗaya da rabi yana bacci.  An yi ittafaƙin cewa a wannan mataki ne mafarki yake faruwa yayin da ɗan adam ya ke bacci. A wannan mataki na bacci, Allah cikin ikonsa sai hannaye da ƙafafuwa su sage. Hikimar hakan shi ne kar mutum ya dinga ayyana abinda yake yi a mafarki da gaɓɓansa a zahiri! 

Rahotannin bincike sun nuna cewa wannan mataki na huɗu na da alaƙa da yadda ake adana bayanai a ma’ajiyar ƙwaƙwalwa. Ƙwaƙwalwar mutum tana da taskoki, wajen adana bayanai guda biyu; a ciki ta ke adana duk abinda ka ji ko ka gani, ko ka koya, ko ya sameka. Taska ta farko ana kiranta Ma’ajiyar Wucin-gadi ko “short term memory” a turance. Yanzu haka da ita kake/kike amfani wajen karantawa da ganewa da fitar da ma’anar abinda nake faɗa a wannan rubutu. Duk tsawon wuni, da wannan taska muke amfani mu adana bayanan abubuwan da suka gifta ta rayuwarmu. 

Taska ta biyu kuwa ita ce Ma’ajiyar Dundundun. Bature ya na kiranta da “Long term memory”. A cikinta mu ke adana bayanai na abubuwan masu muhimmanci,  da abubuwan suka taɓa rayuwarmu sosai, ko suka sosa ranmu, ko suka faranta mana rai sosai. Duk wani abu da ya same mu, na farin ciki ko akasin haka wanda ba zamu taɓa mantawa da shi ba, to haƙiƙa ya na taskance cikin wannan Ma’ajiyar ta Dundundun. 

Ana ɗaukar bayanai na abubuwan da suka faru garemu a cikin wuni daga ma’ajiyar wucin-gadi izuwa ta dundunun lokacin da muka shiga mataki na 4 na bacci ne. Wannan shi yasa a ke bawa ɗalibai shawara da su yi bacci,  kada su yi wasa da shi; domin kuwa a cikin baccin ne ake taskance abinda suka koya a cikin wannan ma’adana ta dundundun. To bayan da wa’adin mataki na huɗu ya ƙare, sai kuma cikin ikon Allah baccin ya koma mataki na farko. Daga nan ya gangaro mataki na biyu, zuwa ba uku, a qarshe har zuwa na huɗu. Haka za ayi ta yi har sai ɗan Adam ya farka. 

Shin baccin awa nawa ya kamata ɗan adam yayi? Wannan tambaya ce da masana su ka tafka muhawara a kanta. Akwai masu ra’ayin awa 8; akwai masu ra’ayin awa 6; da sauransu. Amma ni ina tare da wani masani da ya ce mu yi “isasshen bacci”. Saboda akwai bambanci tsakanin mutane, to fa baccinsu ba zai tava zama kai ɗaya ba! Ni baccin awa 5 ne yake isa ta. Akwai wata likita da na sani, baccin awa 8 ta ke yi! Ku ma ya kamata ku auna ku gani, bacci awa nawa ne ya ke isarki/isarka?

Gidauniyar Bacci ta fitar da jadawalin bacci wanda ya game dukkanin matakan rayuwa na ɗan adam. Jarirai da ba su wuce wata 3 ba, su na buƙatar baccin awa 14 zuwa 17. Jarirai ‘yan wata 4 zuwa shekara 1 kuwa su na buƙatar baccin awa 12 zuwa 16. Yara ‘yan shekara 1 zuwa 2, su na buƙatar baccin awa 11 zuwa 14.

Yara ‘yan shekara 3 zuwa 5, su na buƙatar baccin awa 10 zuwa 13. Yara ‘yan shekara 6 zuwa 12, su kuma su na buƙatar baccin awa 9 zuwa 12. Yara da suka shiga shekarun samartaka ko budurci (“teenagers” a turance), su na buƙatar baccin awa 8 zuwa 10. Manya kuwa daga shekara 18 zuwa 65, su na buƙatar baccin awa 7 abinda yay i sama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *