Bacci a jikin ɗan adam (3)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI

’Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkan mu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi da ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Idan kun shirya, bismillah!

Har yanzu dai muna bayani ne akan bacci. Kamar yadda na faɗa a baya, abu ne mai faɗi gaske, Zan dai yi ita ƙoƙarina na kawo muku ɗan abinda ba a rasa ba kawai. Bari in ɗan yi mana matashiya. Na kawo ma’anar bacci, da siffarsa, da nau’o’insa, da ire-irensa. 

Kamar yadda ku ka sani, bacci Hutu ne ga ƙwaƙwalwa da sauran gaɓɓai. Hutu ne ga ƙwaƙwalwa saboda ita ce kan gaba wajen zartar da duk wani umarni na abin da ka ƙudiri niyyar za ka yi. Idan mutum ya na bacci, ƙwaƙwalwarsa ta huta da fassarawa da wanke hotunan abinda ido ya gani; ta huta da tsinkayen da fassara abinda hanci ya ji; haka kuma babu ruwanta da abinda kunne zai ji. Wato wannan fa shi ake Kira da “summun bukumun”, babu ji babu gani. Iko sai Allah!

A lokacin da mutum ya ke a farke, ƙwaƙwalwa ta na yin ayyuka da dama domin tabbatar da cewa mutum ya fahimci yanayin da yake ciki. Duk abinda idanunka suka gani, to ƙwaƙwalwa sai ta fassara shi, ta bashi ma’ana. Haka shima sauti ko na murya, ko na’ura, ko wani abu, ƙwaƙwalwa za ta fassara shi a cikin daƙiƙu kaɗan. Kenan a lokaci guda idan kana farke, ƙwaƙwalwa tana karɓar saƙon ji, gani, ƙamshi ko wari, ɗumamar yanayi, da amintuwar muhallin da kake ciki a dai dai wannan lokaci. Wadannan abubuwa su na gushewa yayin da mutum ya ke bacci, Wanda hakan ke ba wa ita ƙwaƙwalwa hutu.

Sannan kuma Hutu ne fa sauran gaɓɓai ta inda idan mutum ya na bacci to ba zaiyi zance ko magana ba; ba zai yi tafiya ba, kuma ba zai yi damƙa da hannunka, saboda a lokacin bacci duk gaɓɓai sun shika domin su huta bayan sun sha gwagwarmayar wannan wuni.

Ilimin Kimiyya ya nuna cewa a cikin wannan bacci ƙwaƙwalwa tana mayar da hankali ne wajen yi aikace-aikace na musamman irinsu ƙirƙirar hanyoyin sadarwa tsakanin ƙwayoyin halittar ƙwaƙwalwa, abinda a turance ake Kira da “neural networking”, da kuma inganta hadda a cikin ƙwaƙwalwa, da sauransu. 

A satin da ya wuce, na kawo tambaya mai muhimmanci da na fuskanci mai karatu zai yi muradin sanin amsarta, a inda na ce: Shin baccin awa nawa ya kamata ɗan adam yayi? Wannan tambaya ce da masana su ka tafka muhawara a kanta. Akwai masu ra’ayin awa 8; akwai masu ra’ayin awa 6; da sauransu. Amma ni ina tare da wani masani da ya ce mu yi “isasshen bacci”. Saboda akwai bambanci tsakanin mutane, to fa baccinsu ba zai tava zama kai ɗaya ba! Ni baccin awa 5 ne yake isa ta. Akwai wata likita da na sani, baccin awa 8 ta ke yi! Ku ma ya kamata ku auna ku gani, bacci awa nawa ne ya ke isarki/isarka?

Gidauniyar Bacci ta fitar da jadawalin bacci wanda ya game dukkanin matakan rayuwa na ɗan adam. Jarirai da ba su wuce wata 3 ba, su na buƙatar baccin awa 14 zuwa 17.

Jarirai ‘yan wata 4 zuwa shekara 1 kuwa su na buƙatar baccin awa 12 ɗuwa 16. Yara ‘yan shekara 1 zuwa 2, su na buƙatar baccin awa 11 zuwa 14. Yara ‘yan shekara 3 zuwa 5, su na buƙatar baccin awa 10 zuwa 13. Yara ‘ yan shekara 6 zuwa 12, su kuma su na buƙatar baccin awa 9 zuwa 12.

Yara da suka shiga shekarun samartaka ko budurci (“teenagers” a turance), su na buƙatar baccin awa 8 zuwa 10. Manya kuwa daga shekara 18 zuwa 65, su na buƙatar baccin awa 7 abinda yayi sama. 

Yanayin daɗewar baccinka ko baccinki ya na da nasaba da wasu abubuwa da zan lissafo. Akwai yanayin shekaru kamar yadda ku ka gani. A lokacin ƙuruciya, mutum yafi yin bacci da yawa. A lokacin da shekaru su ka ja kuwa, sai yawan baccin ya fara raguwa. Cima ita ma ta na da alaƙa da yanayin baccin mutum. Cin lafiyayyen abinci mai ɗauke da ajin abinci mai gina jiki wato “proteins”, na taimakawa. Kamar yadda za mu gani a nan gaba insha Allah yadda abinci ke da tasiri a jikin ɗan Adam, ajin abinci na “proteins” ba iya Gina jiki su ke ba, har da wasu ayyuka. 

A ƙwaƙwalwar ɗan adam, akwai wani sinadarin “hormone” da ake kira da “melatonin”. Shi wannan sinadari ana tsarto shi cikin jini yayin da jikin ɗan Adam ya fuskanci cewa dare ya fara yi. Saboda haka aikinsa shi ne ya fara saita al’amuran jiki izuwa shirin yin bacci.To shi wannan sinadari Jikinka yana sarrafa shi ne daga abinci mai ɗauke da “proteins” da kaci lo kika ci.

A wannan gavar ya kamata in shaida muku cewa shi jikin ɗan adam ya na da ‘agogo’ Wanda Sarkin halitta ya dasa masa. Shi wannan agogo a ankare yake da lokacin da kake bacci sannan kuma da lokacin da ka Saba tashi. Ko ko babu agogo a hannunka, za ka iya hasashen qarfe nawa? safiya ce ko dare ne? Shi yasa jikin mutum ya kan samu ruɗani idan akayi balaguro saga wani waje izuwa wani wajen inda akwai tazarar lokaci tsakaninsu. 

Duk lokacin da mutum ya samu isasshen bacci, to zai farka da safe ne cike da kuzari, da shirin fuskantar ayyukan wannan Rana. Lokacin da mutum ya farka, Jikinku zai fara tsarto da sinadarin “cortisol” cikin jini, domin ya bi sannan ya shiga cikin ƙwayoyin halittun jiki. Shi ma “cortisol” sinadaran hormone ne mai sanya ɗan adam wartsakewa. Kuma ana samar da shi ne daga ajin abinci ns “proteins”. Kar ku sake rubutuna akan ‘Abinci A Jikin Mutum ya wuce ku!

Gajiya madaidaiciya na sa a samu bacci mai nauyi kuma mai daɗi. Amma gajiya mai tsanani, musamman abinda bature ta ke kira da “stress”, tana rage ingancin bacci, da ɗaftare tagomashin da akan samu daga bacci. A sanadiyyar haka, ɗan Adam zai iya tsintar kansa cikin matsaloli da ke da alaƙa da rashin isasshen bacci.

Yanzu dai kun fahimci yadda wasu abubuwa ke da tasiri ga irin baccin da mutum zai iya samu, musamman cima. Kirana anan shi ne mu yi ƙoƙari mu kula da abubuwan da na faɗa. Idan Allah ya nuna mana sati mai zuwa, za mu shiga bayani akan amfanin bacci ga jiki da lafiyar ɗan Adam, amma kafin nan na ke cewa bissalam.