Badaƙalar Dala biliyan 2.4: Majalisa ta gayyaci Ministar Kuɗi da Malami

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Kwamitin Majalisar Wakilai ta Tarayya da ke binciken zargin badaƙalar kuɗin man fetur har Dalar Amurka biliyan 2.3 ya yi sammacin Ministar Kuɗi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed da takwaranta na Shari’a, Abubakar Malami.

Kazalika, kwamitin ya buƙaci Sakataren Gwamnatin Tarayya ya bayyana a gabansa a matsayin wani ɓangare na binciken da yake yi.

Shugaban kwamitin, Mark Tersee Gbillah, ne ya bayar da umarnin a lokacin zaman da suka yi ranar Talata.

Kwamitin yana bincike ne kan zargin harƙallar sayar da ɗanyen mai kimanin ganga miliyan 48 ga ƙasar China da kuɗinsa ya kai Dala biliyan biyu da miliyan 400 daga 2014 zuwa yanzu.

Mark ya ce sun aike da sammacin ne da nufin sanin irin rawar da Ma’aikatar Kuɗin da sauran hukumomin suka taka a zargin badaƙalar.

Ya ce, “Abin takaici ne cewa Ministan Shari’a da Ministar Kuɗi duk ba sa nan.

“Abin da muka buƙata shi ne su bayyana a gaban kwamitin saboda mun aike musu da buƙatar yin hakan a hukumance, kasancewar galibin abin da muke nema a ma’aikatunsu suke.