Badaƙalar haramta Tiwita: Nijeriya ta gayyaci wakilan Amurka, Birtaniya da Kanada

Kimanin sa’o’i 48 da sukar matakin haramta Tiwita da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ɗauka, gwamnatin ta gayyaci wakilan ƙasashen Amurka da Birtaniya da Kanada a Nijeriya da su bayyana a gabanta.

Sanarwar gayyatar ta fito ne ta hannun Kimiebi Ebienfa na sashen Sanya Ido Kan Suka da Sadarwa na Ma’aikatar Harkokin Waje ta Nijeriya.

A cewar jami’in, “Biyo bayan haramta Tiwita da Gwamnatin Tarayya ta yi da kuma bayanan da wasu jakadu a Nijeriya suka yi a kan batun dakatarwar, an buƙaci in sanar cewa Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyeama ya gayyaci jakadun da lamarin ya shafa zuwa wajen taro da tsakar ranar wannan Litinin a babban zauren taron ma’aikatar.”

Haka nan, gayyatar ta buƙaci halartar ‘yan jarida domin shaida abin da taron zai tattauna.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *