Badaƙalar N2bn: EFCC ta maka ‘yar gidan Sirika a kotu

Daga BASHIR ISAH

Hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC, za ta gurfanar da ‘yar gidan tsohon Minista Hadi Sirika, Fatimah, tare da wasu mutum biyu a kotu a ranar Alhamis.

Ana zargin waɗanda lamarin ya shafa ne da laifin badaƙalar kwangila ta sama da Naira biliyan 2.7 a ƙarƙashin Ma’aikatar Aufurin Jirgin Sama ƙarƙashin jagorancin Sirika.

Gobe Alhamis shi ne zai zama karon farkon da Sirika zai gurfana a gaban Alƙali Sylvanus Oriji a Babbar Kotun Abuja.

Ana sa ran Sirika ya bayyana a gaban kotu tare da wasu mutum uku, ciki har da ‘yarsa Fatima da kuma kamfanin Al-Duraq Investment Ltd kan zargin almundahanar jwangila ta sama da biliyan N2.7.