Badaƙalar tsare Ari: Bayanan ‘yan uwansa sun ci karo da na ‘yan sanda

‘Yan uwan korarren Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa, Barr. Hudu Yunusa-Ari, sun ce Kwamishinan da kansa ya kai kansa Hedikwatar ‘yan sanda don amsa gayyatar da aka yi masa amma ba tsarewa ba kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana.

Sun ce, a ranar 5 ga Mayu ‘yan sanda suka gayyace shi zuwa hedikwatarsu don amsa tambayoyi, amma bisa ra’in kansa ya tafi ofishin a ranar 2 ga Mayu, 2023

“Wani Sanata ne ma ya tuƙa shi zuwa Babban Ofishin ‘Yan Sandan,” a cewar wani ɗan uwan Kwamishinan

‘Yan uwan sun bayyana wasiƙar gayyatar da ‘yan sanda suka aike wa Arin domin tabbatar wa duniya gaskiyar abin da suke faɗa.

Sai dai a hannu guda, bayanan Babban Ofishin ‘yan sandan sun yi hannun riga da na ‘yan uwan Ari.

Domin kuwa, Hedikwatar ta bayyana a cikin sanarwar da ta fitar ranar Talata ta bakin Kakakinta, Olumuyiwa Adejobi, cewar ‘yan sanda sun tsare Hudu Yunusa-Ari.

Sanarwar ta ce ‘yan sanda sun cika hannu da Arin ne a Abuja, inda yake ci gaba da amsa tambaya kan dalilin da ya sa ya yi riga malam masallaci wajen bayyana sakamakon zaɓe alhali ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen yayin zaɓen cike giɓi na gwamnan jihar da ya gudana kwanan baya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda ya ba da tabbacin za a kamo tare da bincikar duk wani da ke da hannu a badaƙalar da kuma ta tabbatar da adalci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *