Bada izinin gwamnati Afakallah ya ci zarafin ‘yan Kannywwod ba – Mustapha Nabraska

Daga AISHA ASAS

Ci gaba daga makon jiya

MANHAJA: Shin kana ganin wannan hukuma zata iya kama ƙasungumin mawaƙi kamar Rarara?

NABRASKA: To magana ta gaskiya, matuƙar hukumar ta kasa kama Rarara, to zai tabbatar ma ka tare suke, duk abin da ya yi da haɗin bakinsu aka yi. Ma’ana duk abin da Rarara ya yi da haɗin bakin shi shugaban aka yi.

Shin ba ka ganin girma da ƙimar shi Rararan ba zata hana iya kama shi ba?

Babu ƙima ga wanda ya taɓa gwamnati. Babu wanda zai iya tava ƙima da daraja ta gwamnati mai ƙima irin ta Kano a ce ya wuce hukunci. Idan an manta, ba gorin gari ba, shi Rarara ba ɗan Kano ba ne. mutumin Katsina ne.

To, zuwa yanzu wa aka taɓa jin ya yi wa waƙar cin mutunci da ya kasance daga Jihar tasa ta Katsina. Duk da cewa ba fata ake yi ba. Babu shi. Amma a Jihar Kano ka taɓa muhibbar mai martaba sarki, ka taɓa martabar Injiniya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ka tava muhibbar Malam Ibrahim Shekarau, yau kuma ka zo ka taɓa ƙimar mai girma mai daraja, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Khadimul Isalam, Muzakari masanin Allah, gogage da yake ibada akan ɓangaren addinin Musulunci.

Ka zo ka ce za ka taɓa muhibbar wannan bawan Allah. Mutumin da labarin tausayi idan kana ba shi kuka yake yi. Gwamnan Jihar Kano, idan kana ba shi labarin tausayi, kuka yake yi da idanunsa.

To amma wasu na ganin su waɗanda ka lissafo da aka yi mu su, sun yi haƙuri ne, sun kawar da kai. Shin shi mai girma gwamna Dakta Albdullahi Umar Ganduje, ba zai ɗauke kai ba kamar yadda suka yi?

To ai shima mai girma gwamna bai yi magana ba har yanzu. Misali, yanzu kamar ire-iren mu da idan an tava mutuncin mai girma gwamna muke fitowa don mu kare ƙimarsa. Idan har shugaban Hukumar Tace Finafinai ba zai iya fitowa ya kare ƙima da darajar mai girma gwamna ba, ni ‘special adviser on positive profagander’ Ina iya kare ƙima da daraja gwamnati da muhibbar ta, domin Allah ya ɗaga darajata, ƙarƙashin mulkin mai girma gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje, don haka babu abin da zan yi na nuna godiyata face kare ƙima da daraja da kuma muhibbar wannan gwamnati mai albarka.

Kwanaki wani abu ya faru da ya ja ra’ayin mutane, inda a wani taro shi shugaban Hukumar Tace Finafinai ya hau kan kujera, amma ‘yan fim da shi mai girma gwamna suka sauke shi daga kan kujerar. Ko za ka iya gaya mana menene ya faru?

To gaskiya na ɗan ji labarin, amma sama-sama ne, akwai mai bada shawara kan sha’anin Kannywood, Malam Khalid Musa, wanda shi aka sa wa kujera a wurin, shi kuma shi Afakallah sai ya je ya zauna a wurin, inda jama’armu ‘yan fim da aka je da su a wurin, suka ga Malam Khalid a tsaye, sai suka yi yunƙurin cewa, idan fa shi Afakallah bai tashi daga kujerar ba, to fa a shirye suke da su bar wurin.

Mu kuma sai muka ga cewa, kar a ji kunya, a ce, an taru za a yi ‘dinner’ da mai girma gwamna, amma mutane su fice daga taron, kaga wannan abun babu girma, to shi ya sa shi mai girma gwamna ya dubi maslaha a lamarin, kasancewar a kullum shi mai girma gwamna yana kallon menene maslaha a tsakanin al’umma, amma ban san abin da ya faru ba, amma dai na ga shi Afakallah ya miƙe, da ɗan abincinsa da kuma fruit ɗin sa, ya koma kujerar ƙarshe ya zauna, ya juya wa mutane baya don ma kar aga fuskarsa.

Shin wacce irin matsala ce ya samu da ‘yan fim har suke yi masa irin wannan ƙyamar?

To, wato ita al’umma, duk kujerar da aka ɗauko ka, aka baka don al’umma, na farko kar ka saka son zuciya, kar ka yi ‘political attacking’, ka dinga cin zarafin mutane a siyasance. Kar ka mayar da ko wane hukunci naka ɗauri. Komai aka yi ɗauri kawai.

To fa idan har ka bari mutane suka fahimci duk iya hukuncinka zai tsaya ne kan ɗauri, to fa ba za su ji tsoron ka ba, don sun san abin da kawai za ka yi masu kenan, ɗauri ne na gobe, jibi za su iya fitowa.

Wannan ya ja mafi yawa daga mutanen da yake shugabanta suna zuwa nan ofishina, suna kawo ƙorafe-ƙorafen su kan abubun da wannan bawan Allah ya dinga yi.

To yanzu an kawo lokacin da ake buƙatar su mutanen, amma za ka ga duk wanda muka yi ‘inviting’ za ka ji ya ce, in ban da mu ne da ba zai zo ba. Inda don ta wane ne da ba zai yi ba.

To kinga abin da wanen nan ya yi idan alheri ne shi zai kawo mutane, haka za idan sharri ne shi zai kori mutane. Wannan yana daga abinda ya sa idan ka kasa ‘yan Kannywood ɗari, kasha 75 wannan mutumin bai zauna da su lafiya ba.

To kenan gaskiya ne da ake cewa a wancan lokacin wannan al’amari ya janyo saɓani tsakanin gwamnati da su ‘yan Kannywood?

Eh to, gaskiya a wancan lokacin ya bada gudunmawa wurin haddasa tavani tsakanin Kannywood da kuma gwamnati. Saboda kullum jingina wa gwamnati ababen ake, alhali ita gwamnatin ma bata san da rigimar ba, bata san komai ba.

Kawai dai idan ya ɗebo abu sai ya ce, da gwamnati. Wannan ya sa ‘yan Kannywood da kuma masoyansu suka ƙaurace wa gwamnati, don ganin da suke kamar gwamnatin ce ta ke sawa. Amma Allah da ikonSa da Ya kawo mu, muka kuma fahimtar da al’umma cewa, wannan masana’anta da mu muka fito daga cikinta, wannan abu da wannan bawan Allah ke yi maku, gwamnati bata san yana yi ba. Ra’ayinsa ne kawai, don son zuciya irin tasa ko don wani abu da yake tunani.

Mun wayar da kai, kuma mun sunkuyar da kai mun ba su haƙuri. Kamar ni, na yi ƙoƙari wurin dawo da kaso 60 na waɗanda abin ya shafa.

Kana nufin ka ce wannan ne sirrin yadda aka ga ‘yan Kannywood na tururuwar goyon bayan wannan gwamnati?

Wannan gaskiya ne. shi ne dalilin da ya sa mutane suke tururuwar dawo wa bin hanyar mai girma gwamna, domin sun gano cewa, ba shi da hannu a ababen da aka yi masu, kuma sun fahimci cewa, yana matuƙar ƙaunar ‘yan Kannywood.

Kuma yana ba su gudunmawa daidai gwargwado. Kuma sun fahimci ya san irin gudunmawar da suke bayarwa musamman a ɓangaren a zaɓa ko kar a zaɓa.

Na gode.

Ni ma na gode ƙwarai da gaske.