Bai dace Amurka ta cigaba da karya dokokin cuɗanyar ƙasa da ƙasa ba

Daga SAMINU ALHASSAN

Ga alama dai mahukuntan Amurka, na ci gaba da aiwatar da mummunar manufar nan ta muzgunawa kamfanonin ƙasar Sin dake gudanar da halastattun ayyukan su bisa doka.

A baya-bayan nan, gwamnatin Amurkan ta sake ƙaƙaba takunkumin cinikayya kan wasu kamfanonin Sin guda 5, waɗanda ta zarga da cewa wai, suna taimakawa ayyukan soji da na tsaron ƙasar Rasha.

To sai dai kuma, tuni masu fashin baƙi suka fara bayyana rashin dacewar wannan mataki na gwamnatin Amurka, duba da cewa mataki mafi dacewa, shi ne mika wannan batu gaban kwamitin tsaro na MƊD, wanda bisa doka, shi ne ke da alhakin tabbatar da ko waɗannan kamfanoni sun cancanci a ƙaƙaba musu takunkumi ko a’a, amma ba wata ƙasa guda ta aiwatar da mataki bisa raɗin kan ta ba.

Ko shakka babu, Amurka na gwada wani irin misali ga sauran ƙasashe na rashin sanin ya kamata, da nuna ƙarfin tuwo kan kamfanonin sauran ƙasashe ba tare da kiyaye dokokin ƙasa da ƙasa, da na cuɗanyar ƙasashen duniya ba.

A wannan gaba da Amurka ke yi kunnen uwar shegu, da kiraye-kiraye da Sin ke yi mata, na buƙatar hawan teburin shawarwari domin warware sabani, ko ma duk wani nau’in rashin fahimta daka iya bijirowa, idan ƙasar Sin ta maida martani mai karfi, ya zama wajibi Amurka ta dauki alhakin tasirin hakan, a kan ta da ma al’ummar ƙasar sa, wadanda sau da yawa su ne ke ɗanɗana kuɗar mummunan tasirin da hakan ke haifarwa.

Ya kamata mahukuntan Amurka su lura da cewa, rashin jituwarsu da Rasha, ba zai zamo dalili na lalata halastacciyar alaƙar Rasha da sauran ƙasashen duniya ba. Kuma har kullum ƙasar Sin na nacewa kan matsayin ta, na mai ingiza shawarwari da za su kai ga warware rikicin Ukraine cikin lumana, matakin da ya kamata Amurka ta nunawa yabo, maimakon kushe da nuna kiyayya.