Bai kamata a bar ƙasashen Afirka su zama filin ciyayin da manyan giwaye ke faɗa a kai ba

Daga BELLO WANG

Jiya Lahadi, mamban majalisar gudanarwar ƙasar Sin kana ministan wajen ƙasar, Wang Yi, ya gana da takwarorinsa na wasu ƙasashen Afirka, da suka hada da Aljeriya, da Zambia, inda suka tattauna maganar Ukraine. Yayin tattaunawar, ministan wajen ƙasar Aljeriya, Ramtane Lamamra, ya ce, yanzu haka ana keta haƙƙin ƙasashe masu tasowa, ta hanyar tilasta musu ɗaukar wani ɓangare, har ma da yin watsi da ‘yancinsu na tsara manufofin diplomasiyya. Maganarsa ta nuna abun dake ciki zukatan dumbin ƙasashe masu tasowa, musamman ma ƙasashen dake nahiyar Afirka: Yadda ƙasar Amurka da ƙawayenta suke tilastawa sauran ƙasashe saka takunkumi kan ƙasar Rasha, bai dace ba.

Bayan ɓarkewar wutar yaƙi tsakanin Rasha da Ukraine, ƙasar Amurka da wasu kawayenta suna fakewa da kalmar “adalci”, suna ƙoƙarin matsawa ƙasashe masu tasowa lamba, don neman sanya su cikin ƙasashen da suka ƙaƙaba wa ƙasar Rasha takunkumi. Sai dai, tambayar ita ce, shin ƙasar Amurka da kawayenta za su iya wakiltar “adalci”? Dangane da batun, shugaban ƙasar Afirka ta Kudu, Matamela Cyril Ramaphosa, ya tona asirin ƙasar Amurka a kwanan baya, inda ya ce, dalilin da ya sa aka samu ɓarkewar yaki a Ukraine, shi ne yadda ƙungiyar NATO dake karkashin jagorancin ƙasar Amurka, ke ƙara haɓaka ƙarfin ta zuwa gabas cikin shekarun nan. A nan ƙasar Amurka ta yi wayo, inda ta ta da rikici da farko, sa’an nan ta saka wa ƙasar Rasha takunkumi, waɗanda dukkansu matakai ne na dakushe Rasha ɗin.

Ta hanyar saka wa Rasha takunkumi, ƙasar Amurka za ta iya tabbatar da ƙarfinta na yin babakere a duniya, sai dai kuma me wannan mataki zai haifar ga ƙasashe masu tasowa? Mun san ƙasar Rasha tana cikin ƙasashen da suke fitar da ɗimbin amfanin gona zuwa ƙetare. A shekarar 2020, darajar amfanin gona da ƙasashen Afirka suka shigar da su daga Rasha ta kai dalar Amurka bilian 4. Kana ƙasashen Masar, da Sudan, da Najeriya su ne waɗanda suka shigo da mafi yawan amfanin gona daga Rasha. Saboda haka, yadda ake sanya wa Rasha takunkumi zai rage ƙarfin waɗannan kasashen na samar da isashen abinci ga jama’arsu.

Ban da wannan kuma, ƙasar Rasha na samar da ɗanyen mai da iskar gas da yawansu ya wuce kashi 10% cikin ɗaukacin mai da gas da ake samar da su a duniya. Saboda haka, idan an hana ta fitar da mai da gas, hakan zai yi mummunan tasiri kan kasuwannin duniya. Wasu sun ce, hauhawar farashin mai tana da kyau ga ƙasar Najeriya mai samar da mai. Sai dai jama’ar ƙasar Najeriya ba za su yarda da maganar ba, domin har yanzu suna jin raɗaɗin matsalar karancin mai a kasuwannin ƙasar, lamarin da hauhawar farashin mai ta haddasa.

Bugu da ƙari kuma, saka wa ƙasar Rasha takunkumi zai haifar da tasiri kan tsare-tsaren samar da kayayyaki na duniya, da kasuwar hada-hadar kuɗi ta duniya, lamarin da zai tsananta matsalar da ƙasashen Afirka suke fuskanta a fannin tattalin arziki, sakamakon annobar COVID-19. Wato, ja-in-ja da ake yi tsakanin Amurka da Rasha, zai sa jama’ar ƙasashen Afirka shan wahala, wanda kuma hakan sam bai dace ba.

Bayan da ministan wajen ƙasar Sin Wang Yi, ya gana da takwarorinsa na wasu ƙasashen Afirka a wannan karo, ya ce, ƙasar Sin da sauran kasashe masu tasowa sun riga sun cimma matsaya, dangane da hanyar da za a bi wajen daidaita batun Ukraine, wanda ya kasance: A yi ƙoƙarin kawo karshen yaki ta hanyar yin shawarwari cikin sauri, maimakon ɗaukar matakin sanya takunkumi, wanda zai iya bata damar samun farfaɗowar tattalin arzikin duniya. Kana bai kamata a tilastawa wani ɗaukar wani ɓangare ba, domin lamarin zai zama keta ikon mulkin kai na sauran ƙasashe.

Sinawa su kan ce, “ Idan giwaye sun yi faɗa, filin ciyayi zai sha wahala.” Yanzu haka, maganar Ukraine na haifar da tasiri a ɓangarorin siyasa, da tattalin arziki ga wurare daban daban na duniya, kana ƙasashe masu tasowa sun fi jin raɗaɗin rikicin. Har ila yau, komai yanayin da za a shiga ciki, akwai buƙatar tunawa da maganar Wang Yi: Kar a manta da nahiyar Afirka, ko kuma a sake keɓe ta cikin wani bangare, ba tare da lura da ita ba. Sa’an nan, kar a sa ƙasashen Afirka yin hasara sakamakon batun Ukraine din.