Bai kamata Amurka ta qara faɗawa hanyar da ba ta dace ba

Daga CMG HAUSA

A karshen shekarar 2022 da muke ciki, kasar Amurka ta sake rura wuta a kan batun Taiwan. A ranar 24 ga wata, shugaba Joe Biden na Amurka ya sa hannu kan shirin dokar NDAA dangane da kasafin kudi ta fuskar tsaron kasa a shekarar 2023.

Wannan doka ce da Amurka za ta aiwatar a cikin gida, amma Amurka ta fifita dokar fiye da dokokin kasa da kasa. Ta rufe idonta da gangan don kaucewa gaskiya, ta baza jita-jitar barazanar kasar Sin, ta kuma tsoma baki a harkokin cikin gidan kasar Sin.

Dokar tamkar tsoma baki ne kan batun Taiwan, inda aka yi shelar cewa, nan da shekaru 5 masu zuwa, gwamnatin Amurka za ta bai wa yankin Taiwan na kasar Sin tallafin dalar Amurka biliyan 10 ta fuskar aikin soja da kuma rancen kudi na dalar Amurka biliyan 2, za ta kuma bukaci a gaggauta sayar wa Taiwan makamai, lamarin da ba shakka zai taimakawa ‘yan a-ware na Taiwan sosai. Lalle Amurka ita ce wadda ke illata zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan, tare da haifar da barazana ta fuskar tsaro.

Abubuwan da Amurka ta yi kan batun Taiwan sun nuna cewa, tana nuna fuska 2 kan kasar Sin, wadda take yin shelar tattaunawa da kasar Sin tare da dakile ci gaban kasar Sin, kana tana yin shelar hada kai da kasar Sin, tare da illata muraddun kasar Sin.

A yayin ganawar da aka yi tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka a tsibirin Bali a watan jiya, shugaba Biden ya sake nanata cewa, Amurka ba ta goyon bayan kasancewar Sin biyu a duniya, ko kuma kasancewar kasar Sin da Taiwan a duniya. Kana kuma Amurka ba ta neman katse hulda da kasar Sin, ba ta neman dakile ci gaban tattalin arzikin kasar Sin. Kana ba ta neman mayar da Sin saniyar ware.

Abubuwan da Amurka ta yi sun sabawa kalamanta. Ko Amurka ta cancanci kasancewar wata babbar kasa a duniya?

Mai fassara: Tasallah Yuan