Bai wa matasa dama don kawo canji a siyasar Nijeriya

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Lokacin da matashin nan ɗan shekara 25 daga Jihar Kaduna, Muhammad Kadaɗe Suleiman ya fara fitar da fastar neman shugabancin reshen matasan Jam’iyyar PDP, mutane ƙalilan ne suka bai wa takarar tasa muhimmanci, har kuma suke ganin zai iya yin wani tasiri, duk kuwa da ƙarancin shekarun sa. Kasancewar shi ne mafi ƙarancin shekaru a cikin waɗanda suka nemi wannan muƙami na shugabancin Matasan Jam’iyyar PDP ta ƙasa.

Bayanan da suka fito daga dandalin ‘Eagle Square’ da ke Abuja inda aka gudanar da Babban Taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar PDP, an bayyana cewa, Muhammad Kadaɗe Suleiman ya samu nasara ne kan abokin takarar sa Usman el-Kudan da ƙuri’u 3072 daga cikin ƙuri’u 3511 da aka tantance, yayin da ɗan takara na biyu Usman el-Kudan ya zo na biyu da rata mai yawan gaske, inda ya samu ƙuri’u 219.

Ko da yake ba ni da wata masaniya game da wannan matashin ɗan siyasa, amma yadda ya samu tagomashi da ɗaukar hankalin ’yan siyasa, musamman matasa, da suka riƙa bayyana farin cikin su a kafafen sadawa na zamani suna yi masa fatan alheri. Babban abin a yaba ne, wanda kuma har wa yau yake nuna wani sabon sauyi a siyasar ƙasar nan.

Matuƙar manyan ’yan siyasa a ƙasar nan za su riƙa zaƙulo matasa masu hazaƙa suna sa su a gaba da mara musu baya wajen tsayawa takara a muƙamai daban, hakan zai taimaka wajen samar da canji da kawo sauye sauye na dabarun tafiyar da mulki, ƙirƙire-ƙirƙiren abubuwa na kimiyya da fasaha, sakamakon shigar da sabbin jini a harkokin mulki da siyasa.

Salon tsarin mu na cinye-duk da kuma in ba gidana ba sai gidan ’ya’yana, shi ma ya kamata a kawo ƙarshen sa. ’Yan siyasa su tsaya a matsayin su na ’yan siyasa, su zama masu raino da tallafa wa matasa masu tasowa da ke sha’awar tsayawa takara, suna nuna musu abin da ya dace da inda aka yi kuskure don a gyara. Ba zai yiwu a ce mutum ɗaya ya zama kowanne lokaci aka tashi batun takara ko zaɓar wakilci shi ne kaɗai zai fito ba, tun da sauran ƙuruciya har tsufa ya fara bayyana, ya hana sauran masu sha’awa gwada nasu farin jinin, da bayar da tasu gudunmawar.

Tuni dai shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan dokar nan da ta bai wa matasa damar shiga takarar neman wasu muƙaman siyasa, domin ƙarfafa musu gwiwa su shiga a yi da su. Amma a ta bakin matasan samun damar cimma hakan abu ne mai wuya, saboda yadda masu hannu da shuni da manyan ’yan siyasa suka mamaye komai.

Tallafawa matasa a sha’anin siyasa ba ya tsaya ne ga batun ba su shugabanci kan al’amarin matasa kaɗai ba, yana da kyau a riƙa gwada su a wasu muƙaman da aka san suna da basirar da za su tafiyar da shi kuma har su kawo sauyi. Kamar yadda yake a wasu ƙasashen duniya, inda har shugabancin ƙasa ake bai wa matashi dama ya gwada, matuqar ya samu yardar mafi rinjayen ’yan ƙasa, kamar yadda ya faru a ƙasar Faransa, inda matashi Emmanuel Macron ya zama shugaban wannan babbar ƙasa ta Turai yana da shekaru 39, ya kasance shugaba mafi ƙarancin shekaru da aka taɓa yi a ƙasar.

Ban da shi ma akwai wasu matasan da suke taka rawar gani a manyan muƙamai na ƙasashen su, irin su Firaministan ƙasar New Zealand Jacina Ardern mai shekaru 38, ga Firaministan Ukraine Oleksiy Honcharuk mai shekaru 35. Kuma ko a kwanakin nan ma a ƙasar Finland an zavi wata matashiya mai shekaru 34 Sanna Marin da aka zaɓa ta shugabanci ƙasar ƙarƙashin Jam’iyyar SDP, mai ra’ayin kawo sauyi.

A Nijeriya yana da wuya mu amince da jagorancin matasa a muƙaman siyasa da na gwamnati, idan ka ɗauke takarar kansila da aka haƙura aka bar musu, amma ko shugabancin ƙaramar hukuma yana wahala a bar musu, in dai ba ƙaddara ce ta biyo ta kansa ba, kamar yadda a shekarar 2016 tsohon Gwamnan Jihar Legas Akinwunmi Ambode ya naɗa wani matashi ɗan shekara 28 mai suna Gbenga Abiola a matsayin kantoman ƙaramar hukumar Agege. Sai kuma a Jihar Zamfara da aka naɗa ɗan shekara 35 a matsayin kwamishinan Ma’aikatar Ciniki da Masana’antu, Yazeed Shehu Ɗanfulani.
Ana samun ire irensu ɗaiɗaiku nan da can, da in dai ba gata ko sa’a da cancanta ba, yana wuya a ji labarin irin su masu ƙananan shekaru sun haye wani mataki a gwamnatance, ko da kuwa wanda ya shafi rayuwar matasan ne.

A wani rubutu da ya yi a shafin sa na Facebook biyo bayan zaɓen Muhammad Kadaɗe Suleiman, tsohon tsohon Kakakin Gwamnan Jihar Kano Salihu Tanko Yakasai ya bayyana jin daɗin sa da faruwar wannan sabon sauyi na siyasa da aka samu a Jam’iyyar PDP duk kuwa da kasancewar sa ɗan Jam’iyyar APC mai mulki. A cewarsa,

“Wannan abu ya burgeni matuƙa, ganin cewa akwai lokacin da aka samu ɗan shekara 60 a matsayin shugaban matasa na PDP, yau ga shi an samu ci gaba, kujerar matasa an basu abar su. Wannan ba karamin al’amari ba ne a ƙasar nan.”

Ɗawisu, kamar yadda aka san shi da shi ya yi kira ga Jam’iyyar APC mai mulki da ta koyi darasi daga babban taron jam’iyyar adawa ta PDP bisa yadda ta zabo ɗan shekara 25 a matsayin shugaban matasan jam’iyyar.
Mutane da dama sun yi ta bayyana raayoyinsu game da wannan zaɓe daga vangaren ’yan Jam’iyyar PDP har ma da na APC, bisa yadda suke ta nuna lallai lokaci ya yi da za a ƙara jan matasa a jiki da ba su muƙamai da za su ba da gudunmawa da amfani da ƙwarewar da suka samu a makaranta, don kawo sauyi a rayuwa.

Shi ma a nasa ɓangaren shugaban matasan PDP a shiyyar kudancin Jihar Sakkwato Atiku Muhammad Yabo, kira ya yi ga ɗaukacin matasan Nijeriya su fito su marawa sabon shugaban matasan Jam’iyyar PDP na ƙasa, don ya samu ƙwarin gwiwar shigewa gaba ya yi magana da yawun bakin sauran matasan ƙasar nan.

Shugaban matasan kuma Sarkin Samarin Yabo ya yabawa yadda aka samu matasa da suka halarci wannan babban taron suka gudanar da harkokin su cikin lumana da bin doka ba tare da hayaniya ko bankaurar ’yan bangar siyasa ba.

Fatan mu shi ne wannan zaɓe ya zama mabuɗi ga matasan ƙasar nan, na samun qarin dama da ’yancin riƙe wasu muqamai a matakin Jihohi da ƙasa baki ɗaya. Da fatan kuma za su ba mara ɗa kunya, don ganin ba su watsawa ’yan Nijeriya ƙasa a ido ba, sun yi abin da ya dace, wanda kuma zai ƙara nuna matasa na da kishin ƙasa da zuciyar kare martabar al’umma, ba son zuciyar su ba.

Har wa yau kuma ina son na yi amfani da wannan dama na taya sabon shugaban matasan murna, na kuma sanar da shi cewa nauyi ne babba ya hau kansa, domin wakilcin matasan Nijeriya yake yi gaba ɗaya ba na PDP kawai ba, domin nasarar sa za ta iya buɗe wasu ƙofofin da za su bai wa matasa dama a wurare daban-daban.

Don haka ya yi iyakar ƙoƙarinsa domin ganin ya jawo matasan ɓangarorin ƙasar nan kusa da shi, sun yi aiki tare.

Sannan su kuma matasan Jam’iyyar PDP ya zama wajibi ku mara masa baya, da addu’o’i da shawarwari tare da goyon baya, domin ganin ya yi nasara, kar a hantare shi, kar a kafa masa ƙahon zuƙa, idan kuma ya yi kuskure a masa gyara, hakan ne zai sa ya yi nasara ya kuma fidda matasa kunya baki ɗaya.

A nan zan ari shawarar da tsohon kakakin gwamnatin Jihar Kano, Salisu Yakasai, ya bai wa babbar Jam’iyyar APC da ma sauran jam’iyyu cewa, wannan abin misalin da ya faru a PDP wajibi ne ya zama abin koyi a gare su, idan Allah Ya kai mu babban taronta na ƙasa da za a yi a watan Disamba mai zuwa, a tabbatar cewa ba a zavo dattijo a matsayin shugaban matasa ba. Duk wanda za a zaɓo a tabbatar bai haura shekara 35 ba, domin ciwon matashi maganin sa sai matashi. Kujerar matasa a basu a bar su, kar a zo ana angulu da kan zabo!