Baitulmalin Nijeriya ya ƙaru da Dala Biliyan 1.43, inji IMF

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Asusun Nijeriya a halin yanzu ya samu rarar dala biliyan 1.432 a shekarar 2024, a cewar wani rahoto na asusun lamuni na duniya, IMF.

Rahoton ‘World Economic Outlook Database’ wanda gidan talabijin na Channels ya gani a ranar Laraba, ya nuna cewa ƙaruwar asusun gwamnatin tarayya na wannan lokacin, ya kasance ci gaba daga rarar dalar Amurka biliyan 1.21 da aka samu a shekarar 2023.

An danganta wannan ci gaban ne saboda ƙaruwar kuɗaɗen ajiyar ƙasa da kuma zuba jari da ƙasar ke samu.

A shekarar 2024, jimillar kuɗaɗen ajiyar Nijeriya ya ƙaru zuwa kashi 26.32 bisa 100 na kayayyakin cikin gida, daga kashi 24.61 cikin 100 a shekarar 2023. Jimillar jarin kuma ya ƙaru zuwa kashi 25.75 a shekarar 2024, idan aka kwatanta da kashi 24.28 a cikin 2023, a cewar rahoton.

Yana nuna asusun tsakanin fitarwa da shigo da kaya, samun kuɗin shiga da ƙaruwa ko raguwa.

Asusun mai kyau yana nuna matsayi na bada lamuni, yayin da ma’auni mara kyau yana nuna matsayi na aro.

Bayanan na IMF yana ba da kyakkyawan hangen nesa ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya da kwanciyar hankali, yana nuna ci gaban tattalin arziki tare da ƙaruwar saka hannun jari da tanadi. Ana sa ran wannan al’amari zai cigaba, wanda zai haifar da cigaban tattalin arziki da kwanciyar hankali a yankin.

Wannan cigaban dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin da suka biyo bayan cire tallafin da shugaba Bola Tinubu ya yi a watan Mayun 2023.