Baje kolin ƙasa da ƙasa ta hanyar siliki zai zurfafa haɗin gwiwar shirin ziri ɗaya da hanya ɗaya

Daga CMG HAUSA

An buɗe taron baje kolin ƙasa da ƙasa na hanyar silki karo na 6 a Xi’an, babban birnin lardin Shaanxi na Arewa maso yammacin Sin a jiya, inda zurfafa haɗin gwiwa ƙarƙashin shirin Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya za ta kasance babbar ajandar baje kolin.

Baje kolin mai taken karfafa haɗewa da dunƙulewar ci gaba na bai ɗaya da samun sakamakon moriyar juna, ya ja hankalin mahalarta daga sama da ƙasashe da yankuna 70, da suka hada da Jamhuriyar Korea da Thailand da Singapore, inda ƙasar Uzbekistan ke zaman babbar baƙuwa.

Baje kolin na yini 5, zai ƙunshi taruka da dandalin tattaunawa kan maudu’ai kamar na yarjejeniyar haɗin gwiwa da tattalin arziki ta RCEP, da batutuwan raya muhalli da ƙere-ƙeren na’urorin zamani.

Ƙasar Sin ta gabatar da shawarar Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya ne a shekarar 2013, da nufin gina cinikayya da ababen more rayuwa da za su haɗa nahiyar Asia da Turai a kan tsohuwar hanyar cinikin Siliki, domin samun ci gaba na bai daya.

Mataimakin ministan harkokin cinikayya na ƙasar Sin Li Fei, ya ce daga shekarar 2013 zuwa 2021, jimilar kayayyakin da aka yi cinikinsu tsakanin Sin da ƙasashen dake cikin shirin Ziri Ɗaya da Hanya Ɗaya, ya kusa kai Dala triliyan 11, yayin da jari tsakanin Sin da ƙasashen ya zarce dala biliyan 230.

Haka kuma, zuwa ƙarshen 2017, ƙasar Sin ta gina yankunan 79 na haɗin gwiwar cinikayya da tattalin arziki a ƙasashe 24 dake kan hanyar, inda kuma ta zuba jarin dala biliyan 43 tare da samar da guraben ayyukan yi 346,000 a ƙasashen da suka halarci shirin.

Mai Fassarawa: Fa’iza Mustapha