Baje sirrin gidanmu a yanar gizo ba birgewa ba ne

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Wata sabuwa in ji ‘yan caca haka masu magana suka ce. Yau ma ga mu kamar kullum Cikin filinmu mai albarka. Za mu yi magana a kan sabuwar al’adar da ta shigo mana a shafukan yanar gizo, ta kwance sirrin gidajenmu. Yanzu wannan ɗabi’a ta zama kamar ba duniya ce za ta gani ba, idanunmu sun rufe. Ba ga mata ba, ba ga maza ba, wajen baje abunda ya kamata a ce a gida aka yi ko a cikin dangi, a’a, yanzu ɗebowa ake a baje kowa na gani. Ikon Allah! Kuma yawancin wannan rayuwar mata ne suka fi yi, duk da na san ba a rasa nono a riga. Amma shi sirri daɗi ne da shi. Idan miji ya yi miki laifi ya girmi ƙarfin kanki me ya kamata ki fara yi?

Me ya kamata ki yi?

A wajena lallai duk macen da ta kwana ta tashi a cikin gidan aure, ta san  dole ta ga fari da baƙi. Kowacce mace tana da irin damuwarta, wadda kuma ita ya kamata ta magance wa kanta. Idan ta fi ƙarfinta, ta fara zama da mijinta su tattauna kafin wani ya ji ma tukunna. Shi ya sa aka ce zaman haƙuri ne, wanda haƙurin ya fi daɗinsa yawa. Amma haƙuri na iya sa mace ta ci ribar rayuwarta har Duniya da Lahira. Mun jima muna jin haka daga iyayenmu. Da ba mu san ma’anar haka ɗin ba, amma kana shiga gidan aurenka, komai yake sakewa. Lokacin muke tunanin ashe wannan ne abunda iyayen namu suke faɗa (Haƙuri).

Ki fara gyara gidanki:

Ki fara gyara gidanki kafin ki kai wa wani ya gyara. Ƙila ma shi ya riga ki shiga ciki. Wani nasa ma ya fi naki, amma da wuya ya yi kirari ya ɗau wuƙa ya daɓa wa kansa. To komai ɗan haƙuri ne muddin za ki faɗa wa wani, to fa wanin shi ma wani zai gaya wa. Daga nan kin shiga bakin Duniya. Gwara ma kin yi shiru kin gyara wa kanki. Tabbas maza na matuƙar baƙanta wa matansu ta hanyoyi da yawa, wanda yawancin abin cin amana ne. Ka bar matarka ta sunna a gida, ka je kana sabga da wata a waje. Don kawai kana tinƙaho kai namiji ne. Kana da damar da za ka yi abunda kake so. Ka manta amanar da ka ɗauko na kula da ‘yar wani da ka ɗakko matsayin matarka, abar rufin asirinka. Ba wanda zai hana ka, amma ka tuna da nauyin watan da ka raina. Ko za ka yi fitinarka, to ka tuna da Allah ya haramta haka. Ka riƙe mutuncin kanka. Ita ma matarka, ka riƙe mata mutucinta yadda za ta ɗauke ka mutum na ƙwarai, ba mara adalci ba. 

Wayoyi:

Waɗannan wayoyi da muke ɗauke da su yanzu sun fara zama fitina. Ciki maza da mata wasu ke cin karensu babu babbaka har ta kai miji ko mata basa son ɗaya daga cikinsu ya ɗauki wayar ɗaya. Saboda rashin yarda ya shigo ciki. Mace za ta ga badaƙalar da mijinta yake yi. Wala‘alla wata mace daban  a waje, ko cikin ƙawayen matarsa, ko miji ya ga matarsa da wani wanda ya sani, wa’iyazubillah! duk dai sakaci ne kawai daga ma’aurata.Yana da kyau mu ji tsoron Allah, mu gyara wannan fitinar tun kafin gamuwarmu da Allah.

Fitar da sirrin aure:

Wannan ba abu ne mai kyau ba, wallahi. Shi aure ba don wasa aka yi shi ba. Sannan shi ciki ba don abinci kawai aka yi shi ba, har da magana. Amma yanzu mata mun gaza haƙuri, komai ya faru cikin gidanki ko da mijinki ko danginki ko nasa, sai an gaya wa Duniya. Ke wajenki cinyewa ne, wallahi ci baya ne. Shawarar da wanda kika gaya wa kike ganin za su kore miki takaici, wallahi da yawa ƙara miki suke yi. Wasu ma wautar ki suke gani. Ta yaya mace za ta iya fitowa Duniya ta tona wa mijinta asiri? Ba ta ganin yaransu? meye burgewa kin tona wa uban yaranki asiri?
Gidan Duniya dai gidan rikici ne. Duk yadda muka  azuzuwa kala-kala za mu samu. Don haka, kowanne ka zaɓa, da wani a gabansa.

Mutuwa:

Ita kanta yanzu ba a ɗaga mata ba. lokacin da-na-sani.  Mutuwa babbar aba ce idan aka yi wa mutum. Ba wanda aka yi wa mutuwar ba kaɗai, hatta maƙocinka ko wani na jikinka shi ma yi masa aka yi. Amma yanzu gidan mutuwa ya zama gidan biki, gidan gasar abinci, gidan gasar kayan sawa, gidan wawason abinci da zaɓar wanda za a ci. Kai da aka wa mutuwar kawai kai aka yi wa. Kowa sabgoginsa yake yi kaman ba mutuwa ba, ya zama gidan biki.

Maƙabarta:

Ita ma an mai da ita gun hotuna ana tura wa Duniya. Allahu Akbar! Ina za mu kai wannan kayan zunubi da abun kunya? Wasu gasa ma ake ɗauka a hoton a turo ba kunya ba tsoron Allah. Wallahi mu farka daga wannan masifar da muka ɗebo wa kanmu.

Da duk ba mu san wannan ba. Maza ma zaɓar abincin suke a waje. Ga surutu, da zancen Duniya iri-iri kamar ba mutuwa aka yi ba. wasu ma har wanda aka yi wa rashin ake haɗuwa a yi surutu, sai abun ya ba ka mamaki.

Muna ganin kamar cinyewa ne. Wannan abin kunya ne da rashin girmama rashin da muka yi. Ƙiri-ƙiri mun ɗauki al’adar yare mun ɗora wa kanmu. Su ne idan an mutu suke bidi’a iri-iri.To mu ma mun ɗora wa kanmu. marabarmu da su kaɗan ne. Yanzu ba ma sa wa a akwati da kiɗe-kiɗe amma duk sauran abubuwa, iri ɗaya ne. Allah ya sa mu gane, mu daina.

Mun kula da yadda yaran mata ke ɗaukan hotuna marasa kyau suna ɗorawa a instagram ko tik tok. Mun ga Duniya yanzu har da matan aure da mazajen aure suna biye wa ruɗun mata suna abubuwa marasa dacewa. Ka ga dattijo ya bi yarinya ƙarama suna abubuwa na rashin dacewa a matsayin soyayya. Bai duba girmansa da na  iyalinsa ba. Yaya za su ji idan an gan shi a Duniya da ƙaramar yarinya suna abubuwa marasa dacewa? Wallahi mata mu yi wa kanmu faɗa to wacce tarbiyya kenan za mu nuna wa yaranmu?

Mazan aure nagari mu ke ta addu’a Allah ya ba wa yaranmu. Amma fa su matan a duniya da shiga ta rashin mutunci tana nuna wa mazan, ta yaya mazan za su yarda su aure su bayan sun ga yadda suka yi da shiga ta rashin mutunci. da kanmu muka ɓata yaranmu Wallahi. Meye cinyewa a cikin wannan sabuwar fitinar? Baƙin ciki da ɓacin rai har fa da manyan mata. Kai! Wanne ƙarni ne muka shigo? Wallahi mu kanmu matan wani abin kunya muke yi. Ga mata na yi balle kuma yaranmu.

Za mu ɗora sati mai zuwa sha Allahu. Allah ya sada mu da alheri abun da muka yi na dai-dai Allah ya shige mana, wanda muka yi ba na dai-dai ba, Allah ya yafe mana. Bissalam.