Balarabe Musa: Gaba ta wuce…

Daga Ibrahim Sheme

Alhaji Abdulqadir Balarabe Musa mutum ne “wani iri”. Ba a saba ganin irin sa ba. Mutum ne wanda idan an yi Yamma sai ya yi Gabas, idan kuma an yi Kudu shi sai ya yi Arewa. Wasu na kallon sa a matsayin murdadde, ba a yi tanqwasa shi a tattaunawar siyasa; wasu kuma na yi masa kallon mai sauqin kai, mai rungumar talakawa.Ko ma ta wace fuska mutum ya kalle shi, babu wanda zai ce maka ba nagartacce ba ne. Hatta mutanen da ya rayu ya na adawa da manufofin su sun yi ittifaqi da cewa ‘Bala Qaya’ mutum ne tamkar waliyyi, wanda in ka sa masa yatsa a baki ba zai ciza ba.

Allahu Akbar! Alhaji Abdulqadir dai ya yi wafati a ranar 11 ga Nuwamba, 2020, ya na da shekara 84 a duniya. Mutuwar sa ta zo wa mutane a ba-zata, domin yawanci ba a san bai da lafiya ba, duk da yake an dan jima ba a ga fuskar sa a wajen tarurruka ba. Don haka labarin mutuwar ya girgiza kowa. Mutane “’yan Nehu” sun fi kowa kaduwa domin kuwa wani bango nasu ne ya fadi. Rabon da a samu irin wannan rashin a wannan fagen na ‘yan siyasar cigaba ko kawo sauyi, ina jin tun mutuwar Malam Aminu Kano a cikin Afrilu, 1983.

Alhaji Abdulqadir Balarabe Musa ya sha bamban da tunanin yawancin ‘yan siyasar Nijeriya ta fuskar yadda ya ke so a sauya fasalin siyasa domin amfanar talakawa wadanda domin su ne ake riqe ragamar mulki. Ba ma kamar ‘yan siyasar yanzu waxanda yawanci ke cikin siyasar domin abin da za su cika aljifan su da shi, ba domin su kawo waraka ga talaka ba.

Lokacin da ya yi gwamnan Jihar Kaduna daga Oktoba 1979 zuwa Yuni 1981, an ga salon mulkin sa na son talakawa ne. Tun kafin a zabe shi a qarqashin inuwar jam’iyyar PRP ya nuna cewa shi zai yi mulki ne domin talaka, shi ya sa ma ana gama zaben sa ya bayyana cewa gaba dayan mulkin sa ya kafu ne kan ginshiqai biyu: kare haqqin dan’adam da kuma ciyar da al’ummar Jihar Kaduna gaba ta fuskar tattalin arziki. Don cimma wannan manufar, an tsara cewa za a gyara kurakuran da aka tafka a mulki a baya, sannan za a fito da wasu tsare-tsaren domin kafa ginshiqin sabon fasalin siyasa, zamantakewa da tattalin arziki a jihar.

Gwamnatin Balarabe ta yi aiki wurjanjan don cimma burin ta. Ba zan tsaya in jero nasarorin da ta samu ba, irin su soke haraji da jangali, yaqi da cin zarafin dan’adam, ko gina hanyoyi da masana’antu, amma dai abu muhimmi shi ne yawancin ‘yan Majalisar Dokoki ta Jihar Kaduna ba su tare da gwamnan kan irin manufofin sa. Da ma can ‘yan adawa, ‘ya’yan NPN, su ne su ka fi rinjaye a majalisar; shi ya sa kusan duk qudirorin da ya kawo sai su qi amincewa. A qarshe dai su ka tsige shi a ranar 23 ga Yuni, 1981.

Tsige Balarabe ya maida hannun agogo baya a siyasar kawo sauyi a Afrika, domin Balarabe wani misali ne na sabuwar fuskar siyasa da kuma mulki a nahiyar baki daya. In da ya xore a mulki, to da an ga irin alfanun da sauyi zai yi a Afrika, sauyi daga abin da mutane su ka saba gani na mulkin danniya da dintsar hatsi ana watsa wa talaka domin ya dan tsattsaga.

Abin dadin shi ne tsige Balarabe bai canza shi ba kamar yadda zai iya canza wani dan siyasar. Ya ci gaba da zama kaifi daya, bai sauya aqida ba: daga furucin sa na sukar manufofin gwamnati idan ya ga ba za su haifa wa qasa da mai ido ba har zuwa kira da a aikata daidai, da ma zamantakewar sa ta yau da kullum. Ba za mu manta da artabun sa da gwamnatocin Babangida da Abacha ba kan wasu manufofi nasu. Domin ya qi jinin mulkin soja, wata sa’a shi kadai za a ji ya na sukar lamirin soja; kuma ko a mulkin farar hula idan ya ga burbushin wani abu mai kama da sojanci, to yanzu kuwa ya bara. Aqidar sa ita ce bai son rashin adalci da danniya. Ya kan bayyanar da hakan a tarurruka da hirarrakin sa da manema labarai. A kan wannan, bai da tsoro ko gajiyawa. Sannan kudi ko muqami ba su dame shi ba, don haka ba a iya saye shi.

Ya ci gaba da zama dan PRP har qarshe. A yayin da yawancin ‘yan siyasa ke sauya sheqar jam’iyya kamar yadda su ke sauya riga a duk safiya, wannan wani abin yabo ne game da wannan bawan Allah. A zamanin ‘Yar’Adua ya zama shugaban gangamin jam’iyyun siyasar Nijeriya (CNPP) wadda qungiya ce da jam’iyyun adawa su ka kafa musamman don tunkarar wasu nau’o’in danniya da babakere da Hukumar Zave ta Nijeriya (INEC) ta wancan lokacin ta fito da su don maida jam’iyyar da ke mulki ‘yar lelen ta, wato PDP. Balarabe ya yi wa wannan qungiya aiki tuquru wajen wayar da kan jama’a game da duk wata manaqisa da aka shirya don karya lagon siyasar adawa a Nijeriya. Ta haka gwagwarmayar su ta zarce batun INEC kaxai, ta hado har da batun hana juyin mulki, tabbatar da dorewar mulkin dimokiradiyya, kare haqqin ‘yan adawa, da sauran su.

Kusan kowa ya yarda cewa Balarabe tamkar waliyyi ne a badini da zahiri. Na san akwai masu sukar sa kan ya faye kafewa kan aqida, su na cewa ai aqida a siyasa ana sassauta ta domin a kai ga samun madafar iko saboda sai da iko ake iya juya komai. Wasu ma sun ce kafewar sa din nan ta taimaka wajen ganin an tsige shi daga kujerar gwamna.

Shin yau akwai dan siyasa irin Balarabe Musa? Wannan tambaya ta tuno mani da buqatar da Musa Danqwairo ya yi game da Sardauna Ahmadu Bello a wata waqa: “Gaba ta wuce, baya ad da saura, yanzu ku samo wani kama tai”. Amsa tambayar ya na da wuya idan aka yi la’ari da yadda qasar ta koma. Kusan kowa sauri ya ke yi ya wawuri abin da zai iya wawura; ba masu riqe da madafun ikon ba, ba mabiyan ba. Sannan ba kowa ba ne ya damu da halin da talaka ya ke ciki, ko yadda siyasar mu da tattalin arzikin mu su ka tabarbare. A yadda ake tafiya yanzu, duk wanda ya ga wani dan’uwan sa cikin matsi, to sauri ya ke yi ya wuce don kada wani nauyi ya hau kan sa. Ba haka Balarabe ya rayu ba. Shi ya yi aiki da hadisin da ke cewa idan ka ga barna, to ka kauda ita da hannun ka, idan ba ka iyawa, to ka kauda ita da bakin ka, idan ba ka iyawa, to ka qi ta a zuciyar ka. Wa ya ke wannan a yanzu? Ba za a rasa ba, amma fa sai an tona da zurfi, musamman a cikin mutanen da ke qoli.

Don haka samun kamar Balarabe, jan aiki ne. Sai dai mu yi addu’ar Allah ya kawo mana wani kamar sa, shi kuma Allah Ya yi masa sakayya da mafifin alheri.