Ban ɗauki rubutu a matsayin sana’a ba – Muhammad Bala Garba

“Yawaitar marubutan yanar gizo ne ya kashe kasuwar littatafai”

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Filin Adabi a wannan mako ya yi babban ka mu, inda ya samu damar hira da haziƙin marubuci da ya ƙware a harkar rubutu ta fannoni daban-daban, masu bibiyarmu yau mun karɓi baƙuncin Muhammad Bala Garba Maiduguri. A hirarsa da Wakilin Blueprint Manhaja, Ibrahinm Hamisu, za ku ji yadda ya faro rubutu tun daga makarantar sakandire. Ku biyo mu, don jin yadda tattaunawar ta kasance:

MANHAJA: Za mu so ka gabatar da tarihinka ga masu karatunmu?
MUHAMMED BALA: Bismillahir Rahamanir Rahim. Dukkan godiya ta tabbata ga Sarki Allah ƙadimi Mawanji masaɓin halittu bakiɗaya. Tsira da Aminci da Salati da Taslimi su ta tabbatar ga Shugabanmu Annabi Muhammadu (Sallalahu alaihi wasalam). Da iyalan gidansa tsarkaka, da matayensa da sahabbansa da duk waɗanda suka bi shi da kyau da kyautatawa har izuwa ranar sakamako.

Sunana Mohammed Bala Garba. Sunan mahaifiyata Hajiya Asama’u Muhammad Bawayo. Ni Bahaushe ne gaba da baya (uwa da uba). Mahaifina ɗan ƙaramar Hukumar Bunkure ne da ke Jihar Kano. Mahaifiyata kuwa ‘yar ƙaramar Hukumar Warawa ce duk dai a Jihar Kanon. Ni ne babba (na farko) a wajen mahaifiyata; a wajen mahaifina kuma ni ne na shida. An haifi ni a gidan Kakana Alhaji Muhammad Bawayo da ke unguwar Bulumkutu layin Kachalla da ke birnin Maiduguri, a ranar Juma’a, biyu ga watan Rabi’ul Awwal, hijira ta shekarar 1414. Wanda ya yi daidai da 20 ga watan Ogustan 1993.

Na fara da karatun Allo da sauran littatafan Fiƙihu da Sirah da Nahwu da Hadisi da sauran littatafan addini a wajen malamai mabambanta; wanda har yanzu na ke kan yi. Na yi karatun furamare a Kirikassama (Kirikassama primary school) da ke kusa da sakateriyar gwamnatin jihayr Borno ta Musa Usman daga shekarar 1999 zuwa 2005. Na yi sakandire a makarantar jeka-ka-dawo ta Mafoni (Mafoni Government Day Secondary School) da ke kan titin gidan Sir. Kashim; wacce na kammala a shekarar 2011. Na samu shaidar difloma ta farko akan halin zamantakewar rayuwa (Social Work) a Folitekanic ta Ramat (Ramat Polytechnic) da ke birnin Maiduguri a shekarar 2014. Ra’ayin sauya layin karatu ya sa na koma sakandiren Thanawiyatul Sheikh Ahmad Abulfathi (Thanawiyatul Sheikh Ahmad Abulfathi Secondary School) na sake rubuta jarrabawar WAEC a shekarar 2014.

Na samu shaidar difloma ta biyu akan yadda ake sarrafa na’ura mai kwakwalwa (Computer) cikin shekarar 2015 a makarantar kwamfuta ta Yaysib (Yaysib Computer Institute).  Sau biyu ina faɗuwa a jarrabawar kammala Kwalejin Ilimi da Kimiyya ta Haɗa Magunguna da ke Birnin Maiduguri (College of Health Technology Maiduguri), wato a shekarar 2017 zuwa 2019. Na yi difloma ta huɗu akan Arabiyya da Hausa da Addinin Musulunci (Arabic, Hausa & Islamic Study) a Kwalejin Harkokin Shari’a da Addinin Musulunci ta Mohammed Goni a cikin shekarar 2021, duk dai a birnin na Maiduguri.

A yanzu haka Ina zangon ƙarshe (final semester) na kammala digirina na farko a Jami’ar Maiduguri (University of Maiduguri) kan Ilimin Kiwon Lafiya (Health Education). Sannan kuma ina koyarwa a matsayi gudunmawa ga al’ummata (volunteer) a furamaren Mala Kachalla (Mala Kachalla Model Primary) da kuma ƙaramar sakandiren Mafoni (Mafoni Junior Secondary School). Wannan shi ne tarihina a taƙaice.

Ta yaya ka samu kanka a harkar rubutu?
Na samu kaina a harkar rubutu tun ina aji biyu a babbar sakandire (senior secondary 2), saboda a lokacin na ƙware a karance-karancen littatafan. A wannan lokacin, malaminmu na Hausa ya sa mun sayi littafin ‘Jiki Magayi’ da kuma ‘Jatau na Kyalu’ mu na nazarinsu a lokacin darasin Hausa. Duk lokacin da za mu yi darasin Hausa, ni na ke tashi na karanta littatafan, yayin da sauran ɗalibai ‘yan’uwana kuma suke buɗe na su littatafan domin sauraro. Tun daga wannan lokacin na samu kaina a harkar rubutu. Amma ban fara rubuta littafi ba, sai a shekarar 2016.

Me ya ja hankalinka ka shiga harkar rubutu?
Yawan karance-karance shi ya ja hankalina har na shiga harkar rubutu.

Littafai nawa ka rubuta daga lokacin da ka fara rubutu zuwa yanzu?
Daga lokacin da na fara rubutu zuwa yau, na rubuta littatafai kusan goma sha huɗu (14), su ne kamar haka: ‘Shiriya ta Rahamanu 1,2,3’, ‘Tafarkin Tsira’, ‘Sayyadatul Nisa’il Janna’, ‘Ƙasar Borno a Jiya’, ‘Ya Mace a Musulunci’, ‘Gobara daga Kogi’, ‘Burin Zuciya’, ‘Kano ba gari ba dajin Allah’, ‘Manyan Gobe’, ‘Hakimin ban dariya’, ‘Ƙasa ɗaya ƙaddara ɗaya’, ‘One nation one Destiney’, ‘Tarihin Nana Aisha (R.A)’, ‘Bakandamiyata’ (wakokina) da kuma gajerun labarai. Amma littafi ɗaya ne kawai ya shiga kasuwa. Sai littafin ‘Ƙasar Borno a Jiya’ da ake aiki a kansa yanzu.

Ka na rubuta waƙa ne?
Ƙwarai kuwa. Na rubuta waƙoƙi da dama, wanda yanzu haka na kai su sashen nazarin harshe da al’adu na jami’ar Maiduguri domin a duba mini su a gyara su.

Marubuta da yawa sun shiga harkar fim saboda harka ce da ta fi rubutu kawo kuɗi. Shin kai ma ka bi?
Ban bi ba. Hasali ma ni ban ɗauki rubutu a matsayin sana’a ba. Na ɗauki rubutu ne a matsayin hanyar isar da saƙo zuwa ga al’ummar da na ke rayuwa a cikinta. Idan kuɗi ya samu ta hanyar zan yi murna, idan kuma ba su samu ba, daman ban sa haka ba.

Waɗanne irin nasarori ka samu a harkar rubutu?
To, alhamdu lillahi. Domin na samu nasarorin da ba zan iya ƙidaya su ba, sai dai na yi ta yi wa Allah godiya. An karrama ni, an ba ni kyaututtuka, sannan kuma ana mutunta ni da darajanta ni. Bayan haka kuma, na san maza, maza sun sanin. Babu wasu nasarori da suka wuce wannan a rayuwa. Alhamdu lillahi.

Ƙalubale fa; akwai ko babu?
Matsaloli kam ba za su lissafu ba; musamman na rashin kuɗi da zan buga littatafaina. Bayan haka, rashin tsaro da ya addabi yankinmu na Arewa, yana daga cikin manya-mayan matsalolin da mu ke fuskanta a yau. Domin sai da kwanciyar hankali za a samu damar karanta abin da mu ka rubuta ko kuma saƙon da mu ke son isarwa ga wata al’umma zai isa. Bayan wannan kuma akwai rashin samun tallafi daga gwamnati ko ƙungiyoyi masu zaman kansu (musamman ga ƙananan marubuta masu tasowa). Rashin samun ƙarfafa gwiwa daga na gaba da mu ko kuma janmu a jiki duk suna cikin matsalolin da mu ke fuskanta a yau. Uwa-uba kuma shi ne, rashin ba mu damammaki.

Yawaitar marubuta ‘online’ a wannan lokacin cigaba ne ko ci-baya?
Ta wani ɓangaren zai iya zama cigaba, ta wani wajen kuma zai iya zama ci-baya.

Idan ana maganar yaɗuwar adabin Hausa a duniya ne (musamman a yanzu), to marubutan yanar gizo (online writers) sun taka muhimmiyar rawar gani. Domin a dalilinsu rubuce-rubucen Hausa ya shiga wajaje da dama a duniya. Sannan kuma mutane da dama sun iya karatu da rubutun Hausa a yau. Bayan haka kuma, yawaitan yin amfani rubutun Hausa ya fi sauran yarukan yawa a yanar gizo. Idan mu ka koma ɓangaren ci baya kuma, yawaitan marubutan yanar gizo ya kashe kasuwar littatafai. Saboda idan a da (baya) sai ka je kasuwa ka sayi littafi za ka karanta, a yanzu ba sai ka je kasuwa ka siya ba, ga su nan birjik a yanar gizo ba tare da ko kwabo ba za ka karanta. Ga kuma kurakurai sai yawaita suke a faɗin duniya, saboda rashin sanin makamar rubutun Hausa ga mafi yawan marubutan yanar gizo. Uwa-uba kuma ƙyamar da suke janyowa ake yi wa marubuta ko kuma zagi saboda amfani da kalmomi batsa da suke a rubuce-rubucensu. Domin da wuya ka samu ire-iren hakan ga marubuta masu wallafa littafi (amma ban ce babu ba).

Da wanne lokaci ka fi jin daɗin yin rubutu?
Na fi jin daɗin rubutu a duk lokacin da na yi aikin wahala ko doguwar tafiya a ƙas ko kuma na ke cikin gajiya.

Ka taɓa samun lambar yabo a rubutun littafin ko rubutacciyar waƙa?
Ban taɓa samun lambar yabo a rubutun littafi ba; kasancewar littafina ɗaya ne a kasuwa. Dangane da gajerun labarai da waƙa kam, na samu lambar yabo babu adadi.

Da wa ka ke koyi a harkar rubutu?
Ina dai da iyayyen gida, amma batun wa na ke kwaikwayo kam, babu.

Wacce shawara za ka bai wa matasa masu son fara rubutu?
Wanda yake son fara rubutu ko ta ke son fara rubutu ba shawara kaɗai za a ba su ba, shawarwari za a ba su. Shawarata ta farko da zan fara bai wa masu son fara rubutu, shi ne, su yi haƙuri, domin haƙuri shi ne matakin nasara. Dole sai sun yi haƙuri da halin da za su tsinci kansu a harkar rubutu. Domin duk abin da haƙuri bai ba su ba, rashin shi ba zai ba su ba. Waɗansu mutane ba su da haƙuri ko kaɗan, saboda suna da ci da zuci. Babu yadda za a yi daga haifar mutum ya tashi ya ruga a guje. Ɗaukaka ta Allah ce, amma idan an yi haƙuri kuma an jajirce, za a samu. Waɗansu suna shiga harkar rubutu ne don su samu kuɗi; waɗansu kuma don neman ɗaukaka ko kuma su yi suna, yayin da wasu kuma suke shiga domin isar da saƙoninsu ga al’ummar da suke rayuwa a cikinta ko kuma wata al’umma daban. Koma don wanne mutum ya shiga, buƙatarsa za ta biya (In Sha Allahu) amma idan ya yi haƙuri. Shawarata ta biyu da zan bai wa masu son fara rubutu, shi ne, a yi ƙoƙari wajen sanin makamar rubutu. Abin da na ke nufi a nan, shi ne, su yi ƙoƙari su san ƙa’idojin rubutu da ire-iren salon rubutu da zubin da tsari da yadda ake rabe kalma ko kuma haɗe kalmomin da suke haɗe da waɗanda suke rabe. Rashin sanin makamar rubutu shi yake sa idan marubuci ko marubuciya sun yi rubutu, a kasa fahimtar saƙonin na su kwata-kwata ko kuma yadda ya kamata, saboda rashin sanin makamar rubutun. Mu na da Malamai tun daga matakin jami’a har zuwa furamare da dama a wannan harkar, a yi ƙoƙari a nemi wani a mayar da shi uban gida, idan kuna da tambayoyi ko ƙarin haske kan wani abu da ya shige mu ku duhu, ku tambaye shi, zai fayyace mu ku abin da ya shige mu ku duhun.

Abu na gaba kuma shi ne girmama na gaba. Dole idan kuna son cin ribar wannan harkar ko kuma kuna son lamarinku ya yi albarka, ku riƙa girmama na gaba da ku. Hausawa suka ce, ‘Bin na gaba bin Allah’. Don haka dole a girmama na gaba matuƙar ana neman albarkar lamarin. Idan kuka girmama na sama da ku, ku ma wata rana na ƙasa da ku za su girmama ku. Abu na gaba kuma shi ne, a riƙa yin bincike akan duk jigon da za a yi rubutu a kai. Duk jigon da kuka ɗauka za ku yi rubutu akan shi, to ku yi bincike kafin ku fara yin rubutun. Idan za ku yi rubutu akan shari’a, to ku tabbata kun samu masana shari’a kun yi mu su tambayoyi ko kuma kun nemi ƙarin haske akan harkar shari’a. Haka idan akan kiwon lafiya za ku yi, ku samu masana fannin ku yi mu su tambayoyi. Wannan zai sa duk wanda ya karanta labaranku, ya kasa fahimtar ƙiƙiransa aka yi ne, ko kuwa tabbas ya faru da gaske ne. Saboda kun gina labaran da tubalan da suka dace. Sannan kuma a duk lokacin da aka fid da wata gasa, ku yi ƙoƙari ku shiga. Kar ku yi la’akari da yawan waɗanda suka shiga gasar ko kuma zaƙaƙuran da suka shiga gasar, ku shiga ko ba za ku yi nasara ba. Ballatana ma nasara daban, zaƙaƙuranci daban. ‘Sa’a tafi iyawa’ in ji masu iya magana.

Abu na ƙarshe kuma shi ne, a duk lokacin da ku ka kammala rubutu, ku yi ƙoƙari ku kai rubutun na ku ga masana su duba mu ku, domin kaucewa fid da rubutu da kurakurai. Kaso mai yawa na rubuce-rubucen yanar gizo har ma da waɗanda suke kasuwa, cike suke da kurakuran rubutu saboda rashin duba aiyukan idan an kammala. Waɗannan su ne ‘yan shawarwarin da zan bai wa ’yan uwana masu sun fara rubutu.

Mu na godiya.
Ni ma na gode.