Ban ce a zaɓi wani ɗan takara ba baya ga Abba Gida-gida – in ji Kawu Sumaila

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Zaɓaɓɓen sanatan Kano ta Kudu, Suleiman Abdulrahman Kawu Sumaila, ya bayyana cewar ba gaskiya ba ne jita-jitar da ke yawo cewar yana mara wa wata jam’iyya baya a zaɓen gwamna da ke tafe.

Mataimaki na musamman ga Sanata Sumaila a kan yaɗa labarai, Abbas Adam Abbas, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ranar Asabar a Kano

Abbas ya ce, wannan labari ba shi da tushe balle makama.

Ya bayyana cewa wasu masu neman tayar da zaune tsaye gami da yarfen siyasa ne ke yaɗa wannan labari na bogi, inda ya ce a shirye su ke su ɗauki matakin shari’a kan duk mutumin da ke neman ɓata sunan Suleiman Abdul Rahman Kawu Sumaila.

Ya ce Sanata Kawu Sumaila cikakken mai biyayya ne ga jam’iyyar NNPP da ke ƙarƙashin jagorancin Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, a don haka ba zai taɓa furta kalaman da ke nuni da a zaɓi wata jam’iyya ta daban ba a yayin zaɓen gwamna da na ‘yan majalisar jiha.

Sannan sanata Kawu Sumaila ya yi kira ga ɗaukacin al’ummar jihar Kano da su zabi Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan Jihar Kano tare da sauran ‘yan takarar majalisar jiha a tutar NNPP a zaɓen da zai gudana a ranar 18 ga watan Maris.