Ban goyi bayan yaƙar Nijar ba — El-Rufai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gargaɗi Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka ECOWAS da ta dakatar da shirin ɗaukar matakin soji a Jamhuriyar Nijar.

El-Rufai da ya ke bayyana dalilin da ya sa ya ke jan hankalin ECOWAS da ta yi taka-tsan-tsan, ya ce yan Afirka ‘yan uwan ​​juna ne, kuma yakin da ake yi a kowace ƙasa zai yi illa ga kowa.

El-Rufai ya bayyana hakan ne ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, wanda a baya sunansa Tiwita ya bayyana cewa ‘yan ƙasar Nijar da ‘yan Nijeriya mazauna Arewa ɗaya ne.

Tsohon gwamnan ya yi wannan gargaɗin ne biyo bayan sanarwar da shugabannin tsaro na ƙungiyar ECOWAS suka yi iƙirarin cewa ba su da wani zaɓi illa amfani da ƙarfin soji a kan Nijar.

Ƙungiyar ECOWAS ba ta fitar da zaɓin tura dakaru domin tunkarar gwamnatin mulkin Janar Abdoulrahamane Tchiani ba bayan hamɓarar da gwamnatin dimokaraɗiyya ta Shugaba Mohamed Bazoum.

Da yake mayar da martani, El-Rufai ya rubuta cewa, “Yayin da ECOWAS ke buga ganguna na yaƙi, na tuna da 1970s rock classic by Dire Straits – ‘Brothers in Arms’, domin yaƙi a yankinmu yaƙi ne tsakanin ‘yan’uwa. Haƙiƙa al’ummar Jamhuriyar Nijar ɗaya ne da waɗanda ke zaune a Arewacin Nijeriya.

“Don haka mu taka a hankali don guje wa wannan yaqin basasa tsakanin ’yan’uwa.”